| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
’Yansandan Zamfara sun kama matashin da ake zargi da yin kira don 'kai hari Enugu' a wani bidiyo
An ga matashin tare da ɗalibai daga makarantun Islamiyya guda biyu da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar.
’Yansandan Zamfara sun kama matashin da ake zargi da yin kira don 'kai hari Enugu' a wani bidiyo
Kungiyar JIBWIS ce ta mika wa 'yansanda matashin.

Rundunar ’Yansandan Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin wani matashi a cikinsa da yin kiraye-kirayen kashe Kiristoci, tare da tabbatar wa al’umma cewa za ta kare kowa ba tare da nuna bambanci na addini ba.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, A.M. Bello, ya fitar a ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, ya ce bidiyon ya nuna wani matashi sanye da yunifom na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS), reshen jihar Zamfara, wanda ake zargin an ji yana rera waƙar da ke cewa: “Ku ba mu bindigogi mu je mu kashe Kiristoci.”

An ga matashin tare da ɗalibai daga makarantun Islamiyya guda biyu da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar.

’Yansandan sun ce binciken farko ya nuna cewa an ɗauki bidiyon ne a ranar Jumma’a, 23 ga Oktoba, lokacin da ake zargin matashin yana kan hanyarsa ta zuwa Masallacin Aliyu Ibn Abi Thalib, inda shi da wasu suka kasance suna ba da tsaro yayin sallar Jumma’a da wa’azi.

Makarantun da aka danganta da lamarin su ne Nurul Islam Islamiya da Akidatul Sahiha Islamiya, waɗanda dukkansu suke a ƙaramar hukumar Maradun, mai tazarar kusan kilomita 120 daga Gusau, babban birnin jihar.

Rundunar ’yansandan ta ce bayan bayyanar bidiyon, ta tuntuɓi shugabannin JIBWIS na ƙasa da na jihar. Ƙungiyar ta nesanta kanta daga abin da ake zargin matashin ya aikata da kuma abin da ke cikin bidiyon.

Daga bisani, JIBWIS ta kama wanda ake zargin tare da miƙa shi ga rundunar ’yansandan jihar domin gudanar da bincike.

’Yansandan sun bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Umar Ibrahim Gandi Maradun, ɗan Nijeriya kuma haifaffen ƙaramar hukumar Maradun, wanda aka haifa a ranar 15 ga Satumban 2004.

Bayanai na farko sun nuna cewa ya yi karatun firamare a Makarantar Mualledi Model Primary School da kuma sakandare a Government Day Secondary School, dukkansu da ke Maradun.

Ana zargin ya shiga JIBWIS ne a shekarar 2025, sannan kwanan nan ya samu gurbin karatun digiri a fannin sadarwa ta zamani da aikin jarida a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara.

Bincike da matakin shari’a

Rundunar ’yan sandan ta ce tana gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma bayan kammala shi, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ta dace kan zarge-zargen tunzura mutane zuwa tashin hankali, tada hankalin jama’a da kuma yin barazanar aikata laifi.

Ta ce za a yi hakan bisa tanade-tanaden sashe na 77, 78 da 380(b) na dokar Penal Code da ake amfani da ita a jihar Zamfara, gwargwadon hujjojin da binciken zai tabbatar da su da kuma dokokin da suka dace.

Rundunar ta yi Allah-wadai da duk wani aiki da zai iya haddasa ƙiyayyar addini, barazana ga tsaron al’umma ko kawo cikas ga zaman lafiya da zaman tare.

Ta kuma yi kira ga shugabannin addinai, iyaye, masu kula da yara, hukumomin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa koyar da haƙuri, mutunta juna da ɗabi’a nagari, musamman a tsakanin matasa.

Haka kuma, ta shawarci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, sannan su nisanci duk wani abu da zai iya ƙara rura wutar rikicin addini ko kawo cikas ga zaman lafiya.

Kwamishinan ’yansandan ya sake jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma mutunta haƙƙoƙin kowane ɗan ƙasa ba tare da nuna bambanci ba, ciki har da ’yancin tunani, lamiri da yin addini da kundin tsarin mulki ya tanada.

Rumbun Labarai
FBI ta kama mutane tara a Nijeriya da ake zargi da laifukan intanet, an ƙwace na’urori 53
EFCC ta kama ’yan China 14 da ɗan Nijeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba a Ogun
Nijeriya na bibiyar mutum 53 da suka haɗu da mai ɗauke da Ebola a ƙasar, in ji NCDC
’Yanbindiga sun kashe akalla mutane 20 a harin da suka kai wani ƙauyen Jihar Taraba
Shugaba Tinubu na Nijeriya zai kaddamar da yakin neman zabensa yau a Kaduna
Kotun Nijeriya samu mutum 653 da laifin ta’addanci bayan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da su
Gwamnatin Nijeriya ta amince da shirin kwanaki 90 na rage raɗaɗin tsadar rayuwa
Ebola: Nijeriya ta yi kira a kwantar da hankali, ta ce an dakile yaduwar cutar
Kotu ta yanke wa mutumin da ya kashe matarsa hukuncin kisa a jihar Yobe ta Nijeriya
Amurka ta yaba wa NDLEA kan gano wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi masu alaƙa da ƙungiyoyin Mexico
Mun shirya wa zaɓukan Nijeriya na shekarar 2027, in ji INEC
Ebola ta ɓulla a Nijeriya a karon farko bayan shekaru goma sha biyu
Bankin Lamunin Gidaje na Nijeriya zai ƙaddamar da lamunin sayen gida marar ruwa da tallafin haya
DSS ta gurfanar da mutum biyar gaban kotu bisa zarginsu da garkuwa da 'yan NYSC 20 a Imo
Sojojin Nijeriya sun ce sun kashe 'yanta'adda 103 cikin kwanaki takwas a arewa maso gabashin ƙasar
Shugaba Tinubu ya karɓi kwafin daftarin kasafin kuɗin MDD na 2027
‘Alinciba’: Yadda mata a Arewacin Nijeriya ke yaƙi da matsalar bashin da ke saka su a 'masifa'
An samu mutum 11,000 da ke fama da cutar tarin fuka a Jihar Filaton Nijeriya
Sojojin Nijeriya takwas sun rasu bayan motarsu ta taka nakiyar da aka dasa a kan titi
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yanbindiga a Kano tare da ƙwato kudin fansa