Yadda ɗaukar ciki da haihuwa ke zama babbar barazana ga miliyoyin mata marasa galihu

Labarai daga mata a ƙauyuka na fito da irin ƙalubalen da matan ke fuskanta a lokutan da suke da ciki da lokutan haihuwa musamman a nahiyar Afirka da Asia.

By
MDD ta yi gargaɗin cewa a kowane minti ɗaya aƙalla mace ɗaya na mutuwa sakamakon matsalolin haihuwa a faɗin duniya / MSF

Hermina Nandode na zaune a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya (CAR), Murjanatu a arewacin Nijeriya, yayin da Sabera ’yar gudun hijirar Rohingya ce a Bangladesh. Ko da yake suna rayuwa a wurare masu nisa da juna, gwagwarmayar da suka fuskanta saboda juna biyu ta haɗa su.

'Na yi tafiya daga karfe biyar zuwa tara na safe. Dole ne na zo ni kaɗai—iyayena suka iso washe gari. Mijina yana son ya zo amma kekensa ya lalace,' in ji Hermina a tattaunawarta da TRT Afrika, tana rungumar jaririnta da aka nade cikin zane mai launuka.

Tana magana daga asibitin Batangafo a arewacin CAR, inda wasu mata suke tafiya har kilomita 100 don samun kulawar lafiya yayin da suke da juna biyu.

'Matsaloli suna farawa ne da rashin samun damar kula da ciki saboda karancin cibiyoyin lafiya,' in ji Nadine Karenzi, shugabar ɓangaren kiwon lafiya ta Médecins Sans Frontières (MSF) a Batangafo.

'Sannan akwai tazara tsakanin kauyuka da cibiyoyin lafiya, rashin sufuri, rashin tsaro, da kuma kudin tafiya.'

Wasu cibiyoyin lafiya suna aiki ne har zuwa yamma. Kuma a wasu lokuta, saboda rashin tsaro, babu ma'aikatan da suka samu horo ko magunguna da za a ba wa marasa lafiya.

A arewacin Nijeriya, Murjanatu tana jira a Asibitin Gwamnati na Shinkafi da MSF ke tallafawa kafin a a sauya mata asibiti zuwa wani domin magance rashin jinin da take fama da shi.

'Na jinkirta neman magani saboda kudin, ko da don gwaje‑gwajen ciki na yau da kullum. Idan ba ka da kudi, ba za ka iya zuwa awon ciki ba. Babu wanda zai duba ka sai ka biya,' kamar yadda ta bayyana.

Wasu mata suna tafiyar fiye da kilomita 200 zuwa Shinkafi don samun ayyukan MSF kyauta.

Izinin miji

A Cox's Bazar da ke Bangladesh, Sabera ta bayyana makamancin wannan lamarin da ta fuskanta. 'Wani lokaci muna sayar da kayan gida ko aron kudi don mu je asibiti idan buƙatar gaggawa ta taso,' in ji ta.

Yanzu tana dab da haihuwar ɗanta na shida, ta bayyana ɗaya daga cikin ƙalubalen da mata ke yawan fuskanta: 'Wasu mazaje suna ba matansu izinin zuwa asibiti, wasu kuwa ba sa bayarwa.”

'Wata mata na iya ta yi ta shan wahala a gida, ko ma tana zubar da jini ko tana fuskantar mummunan matsala, amma ba za ta iya zuwa asibiti ba sai da izinin mijinta,' in ji Patience Otse, mai kula da ayukan unguwarzoma ta MSF a Shinkafi.

'Wani lokaci ma mijin ba ya gida, don haka dole ta zauna a gida ta jira ya dawo.'

Raquel Vives, wadda unguwarzoma ce kuma ƙwararriya a harkar lafiya ta jima'i da haihuwa tare da Médecins Sans Frontières (MSF), ta ce mutuwar uwa sau da yawa ba a ganin ta, duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗi cewa kowane minti biyu mace tana mutuwa daga matsalolin ciki ko haihuwa.

'Waɗannan ba tarin ibtila'i ne da ba za a iya kaucewa ba – mafi yawan su za a iya daƙile su idan an samu kulawa a kan lokaci,' kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

'Muhimmin abin shi ne tabbatar da cewa mata da yawa yadda ya kamata sun haihu a cibiyar lafiya tare da ma'aikatan haihuwa masu ƙwarewa.

‘Amma a wurare da yawa da muke aiki, babu kayan aiki inda ba su isar har waɗanda suke da matsaloli na haihiwa. Karin yanke tallafin jin kai zai ƙara ƙunci, tare da sanya dubban mata da jarirai cikin haɗari.'

Yawancin matsalolin da ke barazana ga rayukan mata masu ciki da 'yan mata ana iya daƙile. Abubuwan da suka fi yawa sun haɗa da zubar jini, tangarɗa a wurin haihuwa da cututtuka. Rashin gano hawan jini na iya kaiwa ga eklampsiya — yanayi mai haɗari ga rai.

Madina Salittu, wadda unguwarzoma ce a Asibitin Gwamnati na Shinkafi, ta bayyana cewa: 'Wani lokaci hawan jini yana da alaƙa da rashin tsaro, tsoro da damuwa. Yawancin mata ba su da damar zuwa awon ciki kafin haihuwa kuma ba a sa ido kan yanayin hawan jininsu.'

Rashin jini (anaemia) wani babban haɗari ne da ke da alaƙa da matsalolin haihuwa. 'Idan muka karɓi mata 90 masu ciki, akwai yiwuwar 70 za su kasance masu fama da rashin jini, wanda hakan yana ƙara buƙatar sauya jini,' in ji Otse na MSF.

Alida Fiossona tana jiran haihuwar ɗanta na uku a Bignola, wadda wani wurin haihuwa ne da MSF ta kafa kusa da asibitin Batangafo don tabbatar da cewa mata da aka gano suna da haɗari sun samu kulawa cikin lokaci.

Baya ga damuwar lafiya, Alida ta nuna ƙyamar al'umma da yawa da mata ke fuskanta. 'Wasu mutane suna yin wasa da su ko kuma suna ware wadanda suka zo gidan jiran haihuwa. Amma lafiyata tafi muhimmanci—ra'ayinsu ba shi da muhimmanci.'

Ita ma Otse ta ƙara cewa al'adu na iya zama babbar shinge. 'Idan ka haifa a gida, ana ganinka a matsayin mace mai ƙarfi. Idan ka je asibiti, ba haka ake kallonka ba.'

'Daya daga cikin manyan abubuwan da ake nuna halin ko in kula a kansu waɗanda ke haifar da mutuwar uwa shi ne zubar da ciki ba yadda ya kamata ba.

‘Ko da bai kai ga mutuwa ba, amma zai iya haifar da matsaloli na dogon lokaci kamar rashin haihuwa da ciwo wanda zai jima.

‘A cikin ayyukanmu da yawa, muna yawaita jinyar mata waɗanda suka zubar da ciki da kansu waɗanda ke cikin mawuyacin hali,' in ji Vives.

'A cikin yanayin da muke aiki, dokoki masu takura, kyama da rashin damar samun magungunan hana daukar ciki suna tilasta mata zuwa hanyoyin zubar da ciki da kansu.'

Harshe ko yaren da ake magana da shi, shi ma wani ƙarin shinge ne. Emmanuelle Bamongo, wadda unguwarzoma ce a asibitin Batangafo da MSF ke tallafawa, ta bayyana cewa yawancin mata ba sa son zuwa gidan haihuwa saboda tsoron a yi musu dariya don rashin iya magana da harshen Sango, yaren da ya fi rinjaye.

Wannan shi ne halin da Honorine ta kasance a ciki; ta taba daukar ciki sau goma, amma yara shida kacal ne suka tsira. Yanzu a Bignola, karon farko ce za ta je asibiti don haihuwa.

“Bamu da kudi. Don zuwa asibiti, kana bukatar tufafi da na jaririn—amma ba mu iya biya ko da haka ba. Kuma ban iya magana da Sango ba,” kamar yadda ta ƙara da cewa.

Yanke shawararta na neman kulawa ya samo asali ne daga matsalolin da ta fuskanta a lokacin da take da ciki a baya da kuma shawarwarin ma'aikatan lafiya na al'umma da ke kusa da kauyenta.

“Kafin haka, na ji kunya da rashin komai. Amma bayan abin da na gani, idan na sake daukar ciki, zan yi duk abin da zan iya don zuwa asibiti,' ta ƙara da cewa. 'Na ajiye duk wani abu saboda ina son komawa gida da jaririna—mai lafiya.'

“Kafin a kafa wannan gidan haihuwar,” in ji Ruth Mbelkoyo, ma'aikaciyar MSF, “mata da yawa sun rasa jariransu a hanyar zuwa cibiyoyin lafiya masu nisa. Wasu ma sun rasa rayukansu.

‘Ina tuna wata mata daga Kabo [garin da ke da kilomita 60 daga Batangafo] wadda ta rasa cikin farko guda uku. A cikin na huɗu sai ta zo asibiti aka samu ta haifi jariri lafiya.'

Rage jinkiri da shingayen

A shekarar 2024, ma’aikatan MSF a duniya sun taimaka wajen haihuwa fiye da 1,000 a kowace rana—jumullar 369,000. Kashi 15 cikin 100 na waɗannan sun faru ne a Nijeriya, Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya da Bangladesh.

‘Amma aikin ya wuce ɗakin haihuwa: MSF na nufin rage jinkiri da shingayen da ke sa rayukan mata masu ciki cikin haɗari.

“Muna amfani da tsarin kula na rarrabewa,” in ji Otse. “Tawagoginmu ba za su iya isa ga duk matan da ke bukatar mu ba, don haka muna aiki tare da unguwarzomomi da unguwarzomomi na unguwanni waɗanda ke aika maras lafiyar da lamarin ya rikice zuwa cibiyoyin lafiya na matakin farko ko kuma asibiti.”

Vives ta ƙara da cewa: “Idan matsala ta taso, sauri yana da muhimmanci—amma ba ko yaushe za a iya hango su ba.'

“A nan, MSF na magance buƙatu da yawa—daga abinci da magunguna har zuwa tiyata idan an bukata. Haka kuma ana samar da sufuri, zuwa asibiti da kuma dawowa gida,' in ji Madina, wata unguwarzoma a Shinkafi.

Inda ya yiwu, MSF na tallafa wa rumfunan wuraren kiwon lafiya don miƙa mata masu matsala da ke bukatar kulawa, kuma tana aiki da hanyar masu tuka babura don kutsawa wuraren da ke da wahalar shiga a ƙauyuka.

'Muna kuma ƙoƙarin wayar da kan mutane game da tsarin iyali yayin a lokacin awon ciki,' in ji Dinatunessa, wadda unguwarzoma ce a Asibitin MSF na Goyalmara Mother and Child Hospitala Cox's Bazar.

'Muna iya yi wa mata bayani kan fa'idar tazara tsakanin ciki da hanyoyin da ake da su, amma wasu mata ba su da goyon baya daga mazajensu a wannan batun.'

Raquel Vives ta yi tunanin cewa 'mutuwar uwa tana nuna abubuwa da dama da gaba ɗaya ke barazana ga lafiyar mata da haƙƙokinsu—abubuwan da sau da yawa suke ɓoye.

Rashin daidaito tsakanin jinsi yana ƙara tsananta waɗannan haɗurra, domin mata sau da yawa ba su da 'yancin yin shawara, kuɗaɗe, ko ikon yanke shawara da ake buƙata don samun kulawa cikin lokaci da lafiya.

Bayan makonni uku a Bignola kuma bayan ta haifi jaririnta lafiya, Hermina ta yi murmushi. Amma fuskarta ta koma cikin damuwa da wuri.

“Ban sani mai zai faru da uta ba,” inda ta bayyana haka a hankali. “Mace ce.”