| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba fiye da 200
Ana zargin mutanen da hannu a hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar, kamar yadda rundunar ‘yansandan ta bayyana a wani babban aikin haɗin gwiwa da sojoji kan yaƙi da laifuka.
Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba fiye da 200
Afirka ta Kudu ta aika sojoji don yaki da laifuka a yankunan da 'yandaba ke taruwa a Yammacin Cape / Reuters

Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu ranar Talata sun kama 'yan ƙasashen waje fiye da mutum 200 waɗanda galibinsu ba su da takardun zama a ƙasar.

Kana ana zargin su da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar, kamar yadda rundunar ‘yansandan ƙasar ta bayyana a wani samame na haɗin gwiwa da sojoji kan yaƙi da laifuka.

Farmakin da aka kai wata mahaƙa zinare a yammacin Johannesburg yana cikin wani ɓangare na aikin da Shugaba Cyril Ramaphosa ya sanar a watan Fabrairu wanda ya tura sojoji don taimaka wa 'yansanda wajen yaƙi da haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da kuma daƙile rikice-rikicen 'yandaba a wuraren da ake aikata laifuka.

Aikin ya haɗa 'yansanda da sojoji, da kum jami'an tsaro masu zaman kansu, wanda ya kai ga kama mutane 217, kuma sama da 100 daga cikinsu 'yan ci-rani ne daga Lesotho waɗanda ba su da takardun zama a ƙasar, in ji 'yansanda.

Kazalika daga cikin mutanen har da 'yan Mozambique da Zimbabwe da kuma 'yan Afirka ta Kudu, kana an ƙwace makamai da harsasai a wajensu, in ji sanarwar ‘yansandan.

'Shirin Operation Prosper’

A lokacin da aka ƙaddamar da shirin ‘Operation Prosper’, Shugaba Ramaphosa ya ce manyan laifukan da aka tsara, suna "barazana sosai" ga Afirka ta Kudu kana an ware sojoji 2,200 tare da ‘yansada domin gudanar da aikin.

Dubban masu haƙar ma'adinai marasa rijista suna aiki a Afirka ta Kudu, inda suke tono ma'adanai da aka yi watsi da su don neman zinare da sauran ma'adanai a cikin yanayi mai matuƙar haɗari.

Farmakin na ranar Talata ya zo ne yayin da Afirka ta Kudu ke fafutukar daƙile zaman baƙin-haure marasa takardu a ƙasar, inda dubban mutane suka koma gida a cikin 'yan makonnin nan bayan gangamin da ƙungiyoyin cikin gida suka yi waɗanda ke ikirarin cewa 'yan ƙasashen waje suna ƙwace ayyukan yi na 'yan Afirka ta Kudu.