Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya FIFA ta kare shirinta na FIFA Forward Enterprise (FFE) a ranar Jumma'a, a daidai lokacin da hukumomin ƙwallon ƙafa a duniya ke suka da nuna adawa da shirin.
FIFA ta kafe kan cewa "babu wanda zai sayar da ƙwallon ƙafa" kuma za ta ci gaba da shawarwari domin shigar da shirin saka hannun-jari a gasar lashe kofin duniya da sauran wasanni.
A wata sanarwa da ta fitar, FIFA ta ce tana mutunta damuwar da duniya ta nuna game da shawarar kana tana ci gaba da "tattaunawa a bayyane da kuma bin tsarin dimokuraɗiyya."
"An kawo cikas ga tsarin tattaunawarmu saboda rashin sahihancin rahotannin kafofin watsa labarai. Za mu ci gaba da wannan tsari na tattaunawa don tabbatar da cewa an bai wa kowace ƙungiya mambar FIFA damar jefa ƙuri'arta bisa ga gaskiya," in ji FIFA.
Kungiyar ta jaddada cewa an gabatar da shirin FFE ne don ƙara kuɗaɗen ayyukan ci-gaba maimakon mayar da wasan ƙwallon hannun 'yan kasuwa.
"Babu wanda zai sayar da ƙwallon ƙafa. Wannan ba wani abu ba ne da FIFA za ta taɓa lamunta da shi," in ji hukumar.
A ƙarƙashin ƙudurin, za a mayar da ayyukan kasuwanci da shirye-shiryen FIFA zuwa ga wani ɓangare na rukunin FIFA wanda zai ci gaba da zama mallakin FIFA har abada.
Za a raba ƙarin kuɗaɗen shiga na kasuwanci da aka samu tsakanin dukkan ƙungiyoyin mambobi.
FIFA ta ce kowace ƙungiya daga cikin su 211 da ke cikinta za ta samu dala miliyan 20 a cikin tallafin shirin ci-gaban FIFA Forward tsakanin shekarar 2027 zuwa 2030, ba tare da la'akari da ko tana goyon bayan ƙudurin ba.
Kazalika ta gabatar da wani shiri na "sa-kai na lokaci ɗaya", wanda zai bayar da ƙarin dala miliyan 20 ga kowace ƙungiya ta hanyar saka hannun jari na waje.
Hukumar gudanarwa ta FIFA ta kuma jaddada cewa masu zuba jari daga waje ba za su samu iko kan FIFA ko gasanni da take shiryawa ba, kana ta ce za a kafa FFE ne kawai idan aka samu amincewar mafi yawan ƙungiyoyi mambobin hukumar.
Kowa yana da 'yancin bayyana ra'ayinsa da kuma neman ƙarin bayani, amma babu wata ƙungiya da za ta iya iƙirarin wakiltar dukkan ƙungiyoyi mambobi 211 na ƙwallon ƙafa a duniya," in ji FIFA.
Sanarwar ta zo ne kwana ɗaya bayan da ƙungiyoyi 55 na UEFA suka goyi bayan ƙaurace wa gasar FIFA idan hukumar gudanarwarta ta ci gaba da shirin sayar da sha'awar mallakar gasar lashe kofin duniya da sauran gasanni ga masu zuba jari masu zaman kansu.
Bayan wani taron gaggawa, UEFA ta yi gargaɗin cewa babu wata ƙungiyar mamba da za ta shiga shirin gasanin FIFA, sai dai idan hukumar ta yi watsi da shawarar, tana mai bayyana cewa: "Kofin Duniya ba na sayarwa ba ne."
Kazalika taƙaddamar ta ƙara muni a ranar Alhamis bayan da Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta yankin Arewa da Tsakiyar Amurka da kuma Caribbean (CONCACAF) da ƙungiyoyin mambobi 41 suka yi watsi da shawarar, suna masu nuna damuwa kan shugabanci da gaskiya da kuma rashin bin ƙa'ida, gami da abin suka bayyana a sanarwa ta “ɗan karamin lokaci " da rashin bita daga hukumomin FIFA.
FIFA ta ce za a ci gaba da shawara, kuma kofa a buɗe take ga gyare-gyare da amincewa ko ƙin amincewa yayin da ake ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin mambobi a faɗin duniya.



















