Shugaba Bola Tinubu ya shaida wa mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen 2027 na Jam’iyyar APC cewa kada su tsammanci cewa zai bi su ko wane wurin yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa zai mayar da hankali kan jagorancin ƙasar.
Tinubu ya bayyana wannan ne a ranar Laraba dadaddare a wata liyafar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC na zaɓen 2027 a Abuja, inda ya yi kira ga mambobin su kai saƙon jam’iyyar ga ‘yan Nijeriya a faɗin jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar yayin da shi zai ci gaba da mayar da hankali kan batutuwa na tafiyar da ƙasa.
Shugaban ya ce ya amince da kiran da aka yi masa cewa bai kamata yaƙin neman zaɓe ya ɗauke hankalinsa daga jagorancin ƙasar ba, yana mai ƙarawa da cewa Nijeriya na buƙatar hankalinsa a halin yanzu fiye da kowane lokaci a baya.
“Kun mini gargaɗin cewa kada na bari wahalar yaƙin neman zaɓe ta ɗauke hankalina daga jagoranci. Na ji ku. Na yarda 100 bisa 100 da hukuncin da kuka yanke. Nijeriya na buƙatar ƙarin mayar da hankali a halin yanzu,” a cewar Tinubu.
Ya shaida wa mambobin kwamitin cewa su yi masa gafara na bin su duk wani gangamin yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa gwamnatinsa na da kuɗaɗe da kuma buƙatun ƙetare da za ta biya.
“Saboda haka, za ku mini gafara daga bin ku ko ina, muna da kuɗaɗen da za mu biya. Masu binmu basussuka a Amurka ba za su iya jira ba,” in ji shugaban ƙasar.
Tinubu ya kuma ce gwamnatin na buƙatar janyo hankalin ‘yan kasuwa waɗanda za su zuba jari na dogon zango a Nijeriya da kuma ba da gudunmawa a kan makomar yaran ƙasar.
Sai dai kuma shugaban ƙasar ya shaida wa ‘yan Nijeriyar cewa zai ci gaba da magana da su kai-tsaye yayin da kwamitin yaƙin neman zaɓen ke jagorantar kamfe ɗin a faɗin ƙasar.
“Sai dai kuma, zan ware lokaci na magana da ‘yan Nijeriya kai-tsaye, yayin da kuke jagorantar kamfe a jihohi da ƙananan hukumomi,” in ji shi.
Tinubu ya bayyana ƙaddamar da kwamitin a matsayin abin da ya fi yaƙin neman zaɓe kawai, yana mai bayyana shi a matsayin wata alama ta sabunta jajircewa ga Nijeriya da kuma nauyin da ya rataya a kan jam’iyya mai mulki.
“Ba mu taru a nan domin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe ba kawai. Mun zo nan ne domin sake sabunta alƙawarinmu ga Nijeirya. Wani alƙawari da ‘yan Nijeriya da kuma wani nauyi na tarihi da ‘yan Nijeriya suka ba mu amanarta a matsayinmu na jam’iyya mai mulki ta Nijeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ana tsammani kwamitin ya bayyana nasarorin gwamnatin da abubuwan da take hangowa ga masu kaɗa ƙuri’u a faɗin ƙasar.





















