An kama ‘yan ta’addar Daesh sama da 350 a fadin Turkiyya: Ministan Harkokin Cikin Gida
Kimanin ‘yan ta’adda 41 na da alaka da rikicin da ya afku a ranar Litinin a lardin Yalova kuma suna shirin kai irin wadannan hare-hare a Istanbul a lokacin bukukuwan Sabuwar Shekara, in ji mahukunta.
An kama jimillar wadanda ake zargi 357 a fadin turkiyya a wani bangare na ayyukan yaki da kungiyar ta'adda ta Daesh, in ji Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar Ali Yerlikaya a ranar Talata.
A cikin wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta na NSosyal na Turkiyya, Yerlikaya ya ce ayyukan yaki da ta'addanci a lokaci guda a larduna 21 sun kai ga samun nasarar kama wadanda ake zargin.
Ya bayyana cewa rundunonin 'yan sanda na larduna ne suka gudanar da ayyukan tare da hadin gwiwar manyan jami'an gabatar da kara na gwamnati, da kuma sashen yaki da ta'addanci na 'yan sanda da kuma sashen leken asiri, yana mai jaddada cewa Turkiyya ba za ta lamunci ta'addanci ba.
Tun da fari a ranar Talata, Ofishin Babban Mai Gabatar da Kara na Istanbul ya ce an kama wadanda ake zargi da zama mambobin Daesh su 110 a birnin.
A ranar Talata da ta gabata, ofishin babban mai gabatar da kara na Istanbul ya ce an kama mutane 110 da ake zargi a birnin.
Sanarwar ta ce 41 daga cikin su na da alaka da 'yan ta'addar Daesh da ke da hannu lamarin ranar Litinin a lardin Yalova, inda aka kashe 'yan ta'adda shida a wani farmaki da jami'an tsaron Turkiyya suka kai musu. Wadanda ake zargin da aka kama a Istanbul suna shirin kai irin wannan hari a birnin a lokacin bukukuwar Sabuwar Shekara.
Wata sanarwar da Ofishin Babban Mai Gabatar da Kara na Ankara ya fitar ta kuma ce ta bayar da sammacin kama wasu mutane 17 da ake zargin ‘yan ta’addar Daesh ne, ciki har da 'yan kasashen waje 11.
Ana tuhumar wadanda ake zargin da kasancewa mambobin kungiyar ta'adda da kuma ci gaba da hulda da yankunan da ake rikici, in ji sanarwar.
Ta ce Hukumar Binciken Laifukan Ta'addanci ta gano wadanda ake zargin ta hanyar nazarin kayan sadarwa da aka kama a lokacin bincike game da ‘yan ta’addar Daesh da aka gudanar a baya.