Attajirin Nijeriya Aliko Dangote na tunanin Kenya a matsayin wurin da zai gina sabuwar matatar mansa a Gabashin Afirka mai iya tace ganga 650,000 a rana, in ji rahoton Financial Times a ranar Lahadi, inda jaridar ta ruwaito labarin dangane da hirar da aka yi da shi.
"Ina so na karkata zuwa Mombasa saboda Mombasa na da tashar jiragen ruwa mai fadi da zurfi," in ji Dangote a cikin hirar.
Rahoton ya zo ne bayan Shugaban Kenya William Ruto ya ce a watan da ya wuce ƙasashen Gabashin Afirka na tattaunawa kan shirin gina matatar mai ta haɗin gwiwa a tashar jiragen ruwa ta Tanga a Tanzania wadda aka tsara bisa misalin ta Dangote na Nijeriya.
Sai dai, Dangote a cikin hirar ya kwatanta Mombasa ta Kenya da tashar Tanga ta Tanzania, ya ce, "Mutanen Kenya sun fi amfani da mai. Tana da tattalin arziki mafi girma."
Zai iya kashe har zuwa dala biliyan 17
"Komai na hannun Shugaba Ruto," in ji shi.
"Abin da Shugaba Ruto ya ce shi zan yi," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Dangote ya kiyasta cewa gina wannan matatar zai kai dala biliyan 15 zuwa 17, in ji rahoton FT.
A halin yanzu Gabashin Afirka na shigo da dukkan samfuran mai da aka tace, mafi yawansu daga Gabas ta Tsakiya, wanda ke sa yankin fuskantar matsaloli idan aka samu tangardar samar da mai da tashin farashi kamar yadda aka gani yayin yakin Amurka da Isra'ila kan Iran.
Mafi arzikin Afirka, Aliko Dangote, a wani taron tattaunawar ababen more rayuwa a Nairobi a watan da ya wuce, ya ce zai iya yin sak matatar mansa ta Nijeriya a Gabashin Afirka, muddin gwamnatocin yankin sun goyi bayan wannan yunƙuri.
Matatar Dangote mai darajar dala biliyan 20 a cibiyar kasuwanci ta Nijeriya da ke Legas ta fara aiki a 2024.













