Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a ɗaure malaman makaranta shekara 14 kan cin zarafin ɗalibai
Majalisar dattawana Nijeriya ta ce ƙudurin na neman kare ɗalibai daga dukkan nau'in cin zarafi a makarantun gaba da sakandare.
Majalisar dattawan Nijeriya ta amince da wani ƙudirin da ya nemi a yi ɗaurin shekara 14 ga duk malamin makarantar gaba da sakandare da aka samu da laifin cin zarafin ɗalibai.
Matakin yana zuwa ne yayin da ake samun rahotannin cewa malamai suna cin zarafin ɗalibai domin ba su maki da fifita su wajen samun gurbin karatu da kuma sauran fifiko na karatu.
Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar Oyelola Ashiru ne ya gabatar da ƙudurin mai taken “Ƙudirin hana da haramta cin zarafin ɗalibai, shekarar 2025 (HB.1597),” a zaman majalisar na ranar Laraba.
Ashiru ya bayyana cewa an tsara ƙudirin ne domin kare ɗalibai daga duk wani nau’i na cin zarafi ta hanyar lalata a makarantu.
Ya ƙara da cewa an yi ƙudirin ne domin kyautata ɗa’a a makarantun gaba da sakandare da kyautata dangantaka tsakanin ɗalibi da malamai da dogaro da kuma girmama darajar ɗan’adam.
An daɗe ana samun ƙorafi daga ɗaiɗaikun ɗalibai a makarantun gaba da sakandaren Nijeriya kan cin zarafi daga wasu malaman jami’o’i da sauran manyan makarantu na ƙasar.
A wasu lokuta wasu jami’o’in ƙasar sukan kori malaman da aka samu da irin waɗannan laifukan.