| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ɗimbin mutane sun fito kada kuri'a a babban zaɓen ƙasar Zambia
'Yantakara 14 ne ke fafatawa a zaben shugaɓan ƙasar Gambia, ciki har da shugaba Hakainde Hichilema da ke kan mulki .
Ɗimbin mutane sun fito kada kuri'a a babban zaɓen ƙasar Zambia
Tun daga misalin ƙarfe 4 na safe aka fara cika a rumfunan babban zaɓen ƙasar Zambiya

Da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Alhamis ne aka buɗe rumfunan zabe na babban zaben ƙasar Zambia, inda aka samu dimbin masu kada kuri'a da kuma yanayi na kwanciyar hankali.

Haka kuma tun daga karfe 4 na asuba aka soma ganin layukan mutane a rumfunan zabe, inda matasa da wadanda suka manyanta suka fito da kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'unsu.

'Yantakarar shugaban kasa 14, ciki har da shugaban kasa mai ci Hakainde Hichilema, ne za su fafatawa a babban zaben kasar, a wa’adin mulkin tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Hichilema na neman wa'adi na biyu, bayan nasarar da ya samu a shekarar 2021 da kuri'u fiye da miliyan 2.8 wanda ya ba shi damar kayar da shugaban kasa Edgar Lungu na wancan lokacin.

Babban abokin adawan Hichilema

Babban abokin adawan shugaban ƙasar a cikin sauran ‘yantakara 13 a zaben shi ne Brian Mundubile, tsohon minista mai shekaru 55 a gwamnatin jam’iyyar Patriotic Front (PF) wadda ta yi mulki daga 2011 zuwa 2021.

Bayan samun goyon bayan kawancen jam'iyyun adawa, Mundubile ya shiga takarar a watan Mayu kuma yana takara ne a ƙarƙashin sabuwar jam'iyyar NRPUP, wadda ta tattaro goyon bayanta daga jam’iyyar PF.

Kazalika masu kada ƙuri'u za su kuma zaɓi sabbin 'yan majalisa da magajin gari da shugabannin majalisun gundumomi da kuma kansilolin unguwanni.

Ana buƙatar wanda ya yi nasara daga ‘yan takarar shugaban ƙasar ya samu 50 ciki 100 da kuma ɗaya daga cikin jimillar ƙuri'un da aka kada, inda hukumar zaɓe ta ƙasar ta bayyana cewa za a iya sani tare da tantance wanda ya yi nasara nan da ranar Litinin.

Alkawuran yaƙin neman zaɓe

Hichilema, mai shekaru 64, ya lashe zaɓen shugabancin kasar na wa’adin shekaru biyar a 2011 bayan neman kujerar karo na shida kana gangamin yakin neman zaɓensa ya mayar da hankali kan samar da ayyukan yi da kuma wani gagarumin shiri na samar da ababen more rayuwa don tabbatar da sake zaɓe.

Duk da cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 6.8 cikin ɗari a watan Afrilu kuma darajar kuɗin kwacha na ƙasar ta ƙaru, har yanzu mutane da yawa suna fuskantar hauhawar farashin abinci da makamashi.

An daɗe ana kallon ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin mafi kwanciyar hankali a Afirka da ke bin tsarin dimokuraɗiyya.

Zaɓe a Zambia ya saba bin ƙa'idojin yankuna, inda jam'iyyar Hichilema ta fi ƙarfi a yankin kudu da yamma, yayin da jam’iyyar PF kuma ta ke riƙe da madafun iko a yankin arewa da Copperbelt.

Ana sa ran fitowar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a ranar 17 ga Agusta. Sannan ana buƙatar wanda ya yi nasara ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 don guje zuwa zagaye na biyu na zaɓen

Kazalika, masu kada kuri’u za su yin zaɓen ‘yan majalisar dokoki 226 a yanzu, karin da aka samu daga kujeru 156 na baya.


Rumbun Labarai
Fiye da mutum 5000 sun tsere saboda rashin tsaro da ke daɗa ƙamari a Darfur ta Yamma a Sudan: MDD
Daga Chibok zuwa yau: Me ya sa har yanzu makarantun Nijeriya ba su da tsaro?
Hatsarin mota ya kashe mutum 22, ciki har da sojoji 17 a Nijar
An roƙi Chadi ta janye matakinta na ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka
Uganda za ta tura sojoji domin aiki a yankin Gaza
Kenya na binciken abin da ake tunanin guba ce wadda ta kashe giwaye 16
Guinea ta nemi Faransa ta mayar da ƙoƙon kawunan 'yan ƙasarta masu fafutuka
Ƙoƙarin kawar da sankarau: Manufar Afirka ta kawar da cutar baki ɗaya nan da 2030
Mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - Gwamnati
Kwamitin tattaunawa na Libiya ya cim ma matsaya kan tsarin ɗaukar shugaban hukumar zaɓe
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abinci a makare da illolin shan siga da giya
Shugaba Biya na Kamaru ya yi sauye-sauye a shugabancin sojin ƙasar
Ghana ta amince da ɗaurin shekara 20 ga duk wanda ya mayar da gonar koko zuwa wani abu daban
Ɗaruruwan mutane sun yi hijira daga kudu maso yammacin Nijar saboda hare-haren 'yanta'adda
‘Yan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar, in ji kafar watsa labaran gwamnati
Fitacciyar mawaƙiyar Afirka Ta Kudu ta soke kalankuwarta a Legas bayan an kori baƙi daga ƙasarta
Gwamnatin Ghana ta amince da shawara ƙara wa'adin mulkin shugaban ƙasa
Adadin 'yan ci-ranin da suka rasu ya kai 19 bayan dubbai sun tsallaka zuwa yankin Ceuta na Sifaniya
Biranen Afirka 25 da Amurka za ta rufe ayyukan bayar da biza daga ranar 1 ga Agustan 2026
Siyasar Kamaru: Ina Shugaba Paul Biya ya shiga?