TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban Turkiyya ya yi bikin cika shekara 102 da 'yantar da Istanbul daga mamayar abokan gaba
A saƙonsa a ranar Litinin, Erdogan ya miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Turkiyya, inda ya ce an samu nasarar Yaƙin 'Yancin ƙasar ne ta hanyar “sadaukarwar da ba ta misaltuwa daga shahidai da jarumai da suka daraja ƙasarsu fiye da rayukansu”.
Shugaban Turkiyya ya yi bikin cika shekara 102 da 'yantar da Istanbul daga mamayar abokan gaba
Shugaban ya kuma aika saƙon girmamawa ga waɗanda suka yi gwagwarmaya don tabbatar da 'yancin ƙasar
6 Oktoba 2025

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi bikin cika shekara 102 da 'yantar da birnin Istanbul daga mamayar abokan gaba, tare da girmama shahidai da jaruman ƙasa da suka yi gwagwarmayar neman 'yanci.

A cikin saƙon da ya wallafa a ranar Litinin a shafin sada zumunta na NSosyal na Turkiyya, Erdogan ya miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Turkiyya, yana mai cewa an samu nasarar Yaƙin 'Yancin ƙasar ne ta hanyar “sadaukarwar da ba ta misaltuwa ta shahidai da jarumai da suka daraja ƙasarsu fiye da rayukansu,” da kuma “ƙudurin al’ummar Turkiyya na kare 'yancinsu da walwalarsu.”

“Tare da wannan tsarkakkiyar fahimta,” Erdogan ya ce, “muna ci gaba da aiki da ƙuduri mai ƙarfi don karewa da kiyaye Jamhuriyarmu — wadda aka kafa bisa gadon al’adunmu na dā — tare da duk nasarorinta, don ɗaukaka ta sama da matakin al’ummomin zamani, da kuma ƙarfafa ta da sabbin nasarori.”

Shugaban ya kuma aika saƙon girmamawa ga waɗanda suka yi gwagwarmaya don tabbatar da 'yancin ƙasar, inda yake cewa:

“Bisa wannan yardar, ina girmama duk jaruman Yaƙin 'Yancinmu da mutuntawa. Ina sake taya murnar wannan rana mai alfahari ta Istanbul, kuma ina miƙa gaisuwa daga cikin zuciyata ga duka 'yan ƙasarmu.”

An 'yantar da Istanbul a ranar 6 ga Oktoban, 1923, wanda ya kawo ƙarshen mamayar da sojojin ƙawance suka yi na tsawon shekaru huɗu bayan Yaƙin Duniya na Farko, kuma ya buɗe hanya ga ayyana Jamhuriyar Turkiyya daga baya a cikin watan nan.

Rumbun Labarai
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ta wuce $37b ana sa ran ta kai $40b a 2025: Minista
Turkiyya na da rawar da za ta taka a tsaron Turai, ta shirya domin aikin Gaza: Ministan Tsaro
Turkiyya ta yi maraba da amincewar majalisar dokokin TRCN kan ƙudurin samar da ƙasashe biyu
Ya kamata amincewar Ƙasashen Yamma da Falasɗinu ta zama silar samar da mafita ta ƙasa biyu: Erdogan
Jami'an Turkiyya da Syria sun gudanar da tattaunawa kan tsaro a Ankara