Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hidan ya yaba da "Kwamitin Zaman Lafiya" na Gaza

Fidan ya ce kwamitin zai iya taimakawa bukatun jinkai na Gaza da kuma shimfita tushen assasa zaman lafiya dawwamamme.

By
Fidan na goyon bayan "Kwamitin Zaman Lafiya' na Gaza a matsayin hanya ta karshe ta samar da dawwamammen zaman lafiya. / AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce "Kwamitin Zaman Lafiya" na Gaza yana ba da "dama ta tarihi" don samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin da kuma magance wahalhalun da Falasɗinawa ke sha a tsawon lokaci.

Fidan ya rubuta a shafukan sada zumunta a ranar Alhamis cewa, Kwamitin Zaman Lafiya, wanda Shugaba Recep Tayyip Erdogan yake cikin mambobinsa na farko, zai iya taimakawa wajen biyan buƙatun jinƙai na Gaza da kuma shimfiɗa harsashin zaman lafiya mai ɗorewa.

Fidan ya ce ya halarci bikin sanya hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Gaza a Davos, Switzerland, a madadin Shugaba Erdogan.

"Mun yi imanin cewa ta hanyar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da mutanen Gaza, Kwamitin Zaman Lafiya zai taka rawa sosai wajen tsara makomar Gaza, ya taimaka wa yankin ya tsaya kan ƙafafunsa, da kuma barin zaman lafiya ya kafu," in ji shi a saƙon da ya rubuta.

Fidan ya kuma sake tabbatar da matsayin Turkiyya na cewar akwai makomar samar da yanayin da za a saurari bukatun jama’ar Gaza, a kare hakkokinsu kuma su iya zama lafiya.

Fadar White House ta bayyana kama Kwamitin Zaman Lafiya a makon da ya gabata tare da amincewa da Kwamitin Kasa don Kula da Agaza, daya daga cikin kwamitocin da aka kafa don kula da aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Shirin ya samar da matakai 20 da shugaban Amurka Donald Trump ya kawo kuma a watan Nuwmaban bara Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Dinkin Duniya ya amince da shi a mataki na 2803.