| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Ramadan: INEC ta sauya ranakun zaɓen 2027
Bayan hukumar zaɓe ta fitar da ranakun zaɓen 2027 ne dai mutane suka fara ƙorafi game da yadda lokacin zaɓen zai kasance cikin azumin watan Ramadan kuma kusa da ƙaramar Sallah, lamarin da suke ganin zai rage yawan wadanda za su fito zaɓe.
Ramadan: INEC ta sauya ranakun zaɓen 2027
INEC ta sauya ranakun zaɓen 2027 ne bayan ƙorafin da aka yi na kasancewar sun faɗa cikin watan Ramadan kuma kusa da ƙaramar Sallah / AA
27 Fabrairu 2026

Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta sauya ranakun zaɓen shekarar 2027 biyo bayan ƙorafin da aka yi na kasancewar ranakun zaɓen da aka sanar a baya cikin watan azumin Ramadan kuma kusa da ƙaramar Sallah.

A baya dai INEC ta saka ranar Asabar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2027 a matsayin ranar zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yanmajalisun tarayya yayin da ta saka ranar 6 ga watan Maris a matsayin ranar da za a yi zaɓukan gwamnoni da na ‘yanmajalisun jihohi.

Musulmai masu ruwa da tsaki a lamarin zaɓe sun yi watsi da waɗannan ranakun domin sun zo daidai da azumin watan Ramada da kuma kusa da ƙaramar Sallah, lamarin da suke ganin zai rage yawan masu fitowa zaɓe.

Wannan ne ya sa majalisar dattawan ƙasar ta gyara dokar zaɓen ƙasar inda ta rage adadin ranakun da ya zama wajibi hukumar zaɓe ta ba da sanarwar zaɓe daga kwanaki 360 zuwa ranaku 300 , lamarin da ya bai wa INEC damar sauya ranakun zaɓen.

Sabon jadawalin zaɓen da INEC ta wallafa a shafinta ranar Alhamis wanda shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, ya sanya wa hannu ya saka ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2027 a matsayin ranar da za a yi zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yanmajalisun ƙasa yayin da za a yi zaɓukan gwamnoni da na ‘yanmajalisun jihohi ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 2027.