"Ana yin ƙoƙari da gangan don sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya," in ji Shugaban Masar Abdel Fattah el Sisi a ranar Asabar.
"Gabas ta Tsakiya na fuskantar mawuyacin hali a yayin da ake ƙoƙari da gangan na sake zana taswirarta," a cewar Sisi a cikin wani jawabi da aka yaɗa ta talabijin don tunawa da cika shekaru 44 da 'yantar da Sinai daga mamayar Isra'ila.
Ya yi kira a aiwatar da cikakken mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaitawar wuta a Gaza, wacce aka cim ma a watan Oktoban bara, ciki har da shigar da kayan agajin jin-ƙai ba tare da shinge ba, da kuma fara sake gina yankin Falasɗinu nan-take.
Yaƙin kisan kiyashi na Isra'ila da ya shafe shekaru biyu a Gaza tun Oktoba 2023 ya lalata yankin, ya yi sanadin mutuwar sama da 72,500 Falastinawa, mafi yawan su mata da yara.
A mataki na farko na tsagaitawa wuta an yi musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa, amma Isra'ila tana karya sharuɗɗan, ciki har da takaita agaji, da iyakance samun shiga ta Rafah da jinkirta janyewa daga yankin Falasɗinu mai cunkoson jama'a.
Shugaban ya kuma bayyana cikakkiyar kin amincewar Masar da duk wani yunƙuri na korar Falasɗinawa daga wuraren zamansu.

















