| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Ministocin Larabawa sun yi watsi da shirin korar Falasdinawa, suna neman a kare Gaza
Sun yi gargaɗin cewa duk wani tilasta wa Falasɗinawa barin gidajensu zai zama tsarkake ƙabila kuma ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Ministocin Larabawa sun yi watsi da shirin korar Falasdinawa, suna neman a kare Gaza
Ministocin Larabawa sun yi watsi da shirin korar Falasdinawa, suna neman a kare Gaza

Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen Larabawa a ranar Litinin sun yi kira ga a dauki matakin kasa da kasa nan take don kare Falasdinuawa, sannan suka yi yi watsi da duk wani yunkuri na tilasta musu bar kasashensu, suna gargadin cewa irin wannan kora za ta zama tamkar kawar da wata ƙabila kuma take dokar ƙasa da ƙasa ce.

Kiran ya fito ne a cikin ƙudurorin da aka amince da su a karshen taron ministoci na Kungiyar Larabawa a Alkahira, inda ministoci suka yi kira ga al'ummar kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da Majalisar Tsaro, da su dauki mataki kan hare-hareb da Isra'ila ke kai wa kan Falasdinuawa.

Ministocin sun yi kira da a samar da goyon bayan siyasa, kuɗi da na doka ga wani shirin Larabawa da Musulmai na sake gina Gaza, tare da goyon bayan gudanar da taron ƙasa da ƙasa a birnin Alkahira domin tara kuɗaɗen sake gina yankin.

Sun kuma buƙaci a aiwatar da dukkan matakan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma a taron zaman lafiya na Sharm el-Sheikh a shekarar 2025, ciki har da kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila da kuma sake gina yankin.

Ministocin sun yi watsi da duk wani shiri na tilasta wa Falasɗinawa barin gidajensu ko ƙoƙarin sauya tsarin al’ummar yankunan Falasɗinawa da Isra’ila ta mamaye, ciki har da shawarwarin da Isra’ila ke kira da “ƙaura bisa son rai”.

Sun yi gargaɗin cewa duk wani tilasta wa Falasɗinawa barin gidajensu zai zama tsarkake ƙabila kuma ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Ministoci sun yi Allah wadai da mummunan barnar jinƙai a Gaza

Ministocin Larabawa sun kuma yi Allah-wadai da yadda Isra’ila ke gudanar da ayyukanta a Gaza, inda suka bayyana lamarin da cewa ya ƙunshi kisan kare dangi, yunwa, killacewa, laifukan yaƙi da kuma laifukan cin zarafin bil’adama.

A cewar alkaluman da aka gabatar, fiye da Falasɗinawa 73,000 ne aka kashe, yayin da fiye da 174,000 suka jikkata tun bayan fara yakin da aka bayyana a matsayin na kisan kare dangi. Haka kuma, an lalata ko kuma lalace manyan sassan kayayyakin more rayuwa na fararen hula a Gaza.

Ƙudurin ministocin ya sake jaddada muhimmancin kare Falasɗinawa da ke Gaza, hana tilasta musu barin yankin na dindindin, da kuma samar da goyon bayan ƙasa da ƙasa domin farfaɗo da sake gina yankin da ke ƙarƙashin killacewa.