Mbappe ya shiga sahun Ronaldo, Messi, da Lewandowski wajen cin ƙwallaye 60 a shekara guda
Kylian Mbappe na Real Madrid ya shiga ajin gwaninsa tsohon ɗanwasan Madrid, Cristiano Ronaldo, da tsohon danwasan Barcelona, Lionel Messi, da ɗanwasan Barca a yanzu Robert Lewandowski.
Tauraron ɗanwasan Real madrid, Kylian Mbappe ya ci zunzurutun ƙwallaye har 60 a shekarar nan ta 2025.
Wannan bajinta da ya nuna ta sa ɗanwasan ɗan asalin Faransa ya shiga sahun tsirarun zaratan ‘yan wasa a duniya da suka taɓa kafa irin wannan tarihi.
A ƙarnin nan na shekarun 2000, ‘yan wasan da suka yi wannan zarra ba su wuce uku ba.
Su ne Cristiano Ronaldo, tsohon ɗanwasan Madrid, da Lionel Messi, tsohon ɗanwasan Barca, da kuma Robert Lewandowski da ke Barca a yanzu.
Mbappe ya cimma wannan adadin ƙwallaye ne a wasan da Madrid ta buga da Girona ranar Lahadin nan, inda aka tashi canjaras da ci 1-1.
Ko a Faransa ma, rabon da wani Bafaranshe ya ci ƙwallo 60 a shekara tun wani mai suna Just Fontaine a 1958.
Shekarar ta 2025 ta ƙara fito da bajintar Kylian Mbappe wanda ya zo Real Madrid a Yulin 2024, inda ya zamo jagoran cin ƙwallaye a Madrid da gasar LaLiga a yanzu.