| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Yara na cikin waɗanda aka kashe a harin jirgi marar matuƙi a wata kasuwar Sudan
Hukumar MDD ta ce yara na ci gaba da cutuwa daga rikicin da ke kara tsamari a fadin kasar Sudan.
Yara na cikin waɗanda aka kashe a harin jirgi marar matuƙi a wata kasuwar Sudan
Sudan ta fada yakin basasa da har yanzo ya ki kawo wa karshe.

Wani hari da jirgin sama mara matuki ya kai kan wata kasuwa a jihar Kordofan ta Arewa da ke Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane shida, ciki har da yara biyu, tare da raunata wasu sama da 26, in ji Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).

UNICEF sun yi gargadin cewa yara na ci gaba da shan wahala sakamakon rikicin da ke kara ta’azzara a kasar.

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, UNICEF ta ce harin ya nufi wata kasuwa a garin Al-Rahad, inda ya kashe yara biyu da manya hudu, yayin da ya jikkata sama da mutane 20, ciki har da yara shida tsakanin shekaru 6 zuwa 14.

"Wannan sabon harin na tunatar da mummunan tasirin da rikicin ke ci gaba da yi wa yara a fadin Sudan," in ji Wakilin UNICEF a Sudan Sheldon Yett.

"Kasuwanni wurare ne da iyalai ke taruwa don sayen abinci, samun abin rayuwa da biyan bukatunsu na yau da kullum. Bai kamata su zama wuraren mutuwa da halaka ba," in ji shi.

‘Lamari mai matukar ban tsoro’

Yett ya ce tashin hankalin da aka samu kwanan nan a birnin El-Obeid da kewaye, babban birnin Arewacin Kordofan, ya jawo hankalin ƙasashen duniya, amma ya yi gargadin cewa lamarin a faɗin kasar har yanzu yana "da ban tsoro."

Ya ce al'ummomin Dilling da Kadugli a Kudancin Kordofan, sassan Arewacin Darfur, da yankunan Blue Nile da rikicin ya shafa na ci gaba da fuskantar matsanancin rashin tsaro, gudun hijira da kuma buƙatun jinkai.

"Duk inda rikicin ya yaɗu, yara ne suka fi kowa illatuwa," in ji Yett.

A cewar UNICEF, hare-haren da ake yawan kai wa suna lalata gidaje, makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, hanyoyin ruwa da kasuwanni, suna hana yara damar samun kiwon lafiya, ilimi, abinci mai gina jiki, ruwa mai tsafta da tsaftar muhalli yayin da ake tilasta wa iyalai da yawa barin gidajensu.

Hari kan hanyoyin jigilar kayayyaki

Hukumar ta kuma yi gargadin cewa hare-hare da rashin tsaro a manyan hanyoyin samar da kayayyaki suna kawo cikas ga ayyukan jinkai da kuma takaita hanyoyin shiga wasu daga cikin al'ummomin da suka fi rauni a kasar.

"Kowane yaro da aka kashe ko ya ji rauni yana da yawa," in ji Yett, yana mai kira ga dukkan bangarorin da ke rikici da su kare fararen hula da kayayyakin more rayuwa na fararen hula, su bi dokokin jinkai na kasa da kasa, sannan su tabbatar da samun damar shiga ayyukan jinkai cikin aminci, cikin sauri, kuma ba tare da wata matsala ba.

Sudan ta fada cikin yaki tsakanin sojojin Sudan da rundunar sojojin sa kai ta gaggawa tun daga watan Afrilun 2023, wanda hakan ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin jinkai da na 'yan gudun hijira a duniya.

Rumbun Labarai
Rundunar Operation Damissa a Nijar ta lalata maɓoyar mayaƙan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Dosso
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030
Majalisar Sudan ta cire 'yantawayen RSF daga tattaunawar ƙasa
An raba mutane fiye da 4,500 da gidajensu a Darfur ta Kudu da Blue Nile saboda matsalar tsaro
An ceto fiye da 'yan ci-rani 1,000 kusa da tekun yammacin Afirka cikin mako ɗaya, in ji MSF
Shugaban Zambia Hichilema ya yi farin ciki da masoyan da suka ba shi kyautar kazar gida
Gwamnatin Ghana ta kashe $4.37m don kwashe 'yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu
Gwamnatin Nijar ta yi kira ga jama'a su duƙufa da Al-Ƙunut domin neman tsari daga 'maƙiyan ƙasa'
Kwalara ta kashe mutum 23 a Sudan, fiye da 310 sun kamu da cutar
Majalisar Dinkin Duniya ta amince a sake zana taswirar Afirka zuwa ainihin yadda nahiyar take
Nijar na zargin Faransa da tunzura sojojin da suka yi yunkurin tawayen da aka dakile
Tallafin ƙasashen waje da harin jiragen sama marasa matuƙa sun ƙara tsananta yaƙin Sudan - MDD
Babban hafsan sojin Sudan Burhan na rangaɗi game da shirin yaƙi a fagen yaƙin Blue Nile