Erdogan ya gaya wa Pezeshkian cewa tattaunawar Amurka da Iran za ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa

Shugaban Erdogan ya ce Turkiyya da sauran ƙasashen da lamarin ya shafa, sun taka muhimmiyar rawa har zuwa ga tsawon lokacin da aka cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

By
Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi waya da Shugaban Iran Pezeshkian. / TRT Afrika Hausa

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana ta wayar tarho da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian, inda suka tattauna batun tsagaita wuta na wucin-gadi na tsawon makonni biyu tsakanin Amurka da Iran da kuma tsaron yankin.

A cewar wata sanarwa da Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta fitar a ranar Alhamis, Erdogan ya ce Turkiyya, tare da sauran ƙasashen da abin ya shafa, sun yi "ƙoƙari sosai" a tsarin da ya kai ga tsagaita wuta.

Ya yi kira da yi amfani da yarjejeniyar Amurka da Iran wadda za ta fara aiki a cikin kwanaki masu zuwa a Pakistan gwargwadon iyawarsu don cim ma zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa.

Erdogan ya jaddada muhimmancin "rashin bai wa waɗanda ke son yin ɓarna" tsarin zaman lafiya, yana mai bayyana shirin Ankara na samar da "duk wani tallafi da zai yiwu a sabon matakin yarjejeniya."

A yayin wayar da ya yi shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba, Erdogan ya jaddada buƙatar yin amfani da wannan lokacin yadda ya kamata tare da gargaɗi game da duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga tsarin.

A ranar Laraba, Firaiministan Pakistan Shehbaz Sharif ya gode wa Turkiyya, China, Saudi Arabia, da sauran kawayen ƙasarsa saboda "goyon bayan da suka yi mai mahimmanci" don tabbatar da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.

Erdogan ya ce Turkiyya a shirye take ta bayar da duk wata gudummawa da za ta iya bayarwa ga sabon matakin tare da ƙasashe ƙawayenta da abokan hulɗa.

Shugaban na Turkiyya ya kuma yi ta'aziyya kan asarar da "'yan’uwanta na Iran" suka yi.

Kazalika a cikin ‘yan kwanakin nan Erdogan ya yi kiraye-kiraye da dama don hanzarta tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

Iran da Amurka sun sanar da tsagaita wuta na makonni biyu a ranar Talata da nufin share fagen yarjejeniyar karshe don kawo ƙarshen yaƙin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da jikkata dubbai tun daga ranar 28 ga Fabrairu.

Ana sa ran gudanar da zagaye na farko na tattaunawar yarjejeniyar a hukumance a Islamabad ranar Asabar.