Fadar Shugaban Nijeriya ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da waɗanda harin baya-bayan nan a Jihar Filato ya shafa a filin jirgin sama na Jos ne maimakon a cikin gari a ranar Alhamis saboda ƙalubalen tsaro.
A cewar wata sanarwa daga Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga wacce ya wallafa a shafin X ranar Jumma’a, tun da farko Shugaban Ƙasar ya tsara muhimman ayyuka guda biyu a ranar, da karɓar baƙuncin Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Déby Itno a Abuja, da kuma tafiya Iperu a Jihar Ogun.
Sai dai bayan wani bayani da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yi masa kan mummunan harin, Tinubu ya dakatar da tafiyarsa zuwa Ogun tare da shirya kai ziyarar gaggawa zuwa Jos.
“Ziyarar shugaban ƙasar Chadi, wadda ta mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu, ba za a iya ɗage ta ba, kuma ta ɗauki lokaci fiye da yadda aka tsara, lamarin da ya jinkirta tafiyar shugaban zuwa Filato,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa bayan isarsa Jos, wasu ƙalubale sun sake bayyana. Filin jirgin saman ba ya aiki da daddare saboda rashin na’urorin taimakon sauka da tashin jirage, wanda hakan ya sa ba zai yiwu shugaban ya shiga cikin gari, ya gana da waɗanda abin ya shafa, sannan ya dawo filin jirgin kafin duhu ya yi ba.
Saboda haka, jami’an jiha da na tarayya suka shirya a kawo wakilan al’ummomin da abin ya shafa zuwa wani ɗakin taro da ke kusa da filin jirgin domin ganawa da shugaban cikin gaggawa.
Daga cikin waɗanda suka halarta akwai manyan jami’an tsaro, ciki har da Ministan Tsaro, Shugaban Rundunar Sojoji, da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, waɗanda tun da farko suka ziyarci Rukuba, inda rikicin ya fi kamari.
Haka kuma, an tura wata babbar tawaga kafin zuwan shugaban domin tantance halin da ake ciki da kuma tattaunawa da al’umma.
A yayin ganawar, Shugaba Tinubu ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana addabar Jihar Filato.
Ya kuma tabbatar wa al’umma da cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da adalci tare da dawo da zaman lafiya.
Shugaban ya kuma sanar da shirin girke kyamarori 5,000 masu amfani da fasahar basirar wucin gadi (AI) a faɗin jihar domin ƙarfafa tsaro, inganta sa ido, da kuma taimakawa wajen gano da kama masu aikata laifuka.
Haka kuma ya gayyaci shugabannin al’umma zuwa Abuja domin ci gaba da tattaunawa kan hanyoyin samar da mafita mai ɗorewa ga rikice-rikicen da ke maimaituwa.
An bayyana ganawar, wadda aka watsa kai-tsaye, a matsayin mai cike da tausayawa amma kuma mai ƙarfafa gwiwa, inda jami’ai suka ce ziyarar wata dabara ce ta magance tushen matsalolin tsaro da kuma gina zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.








