Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta tabbatar da kashe jami’anta 17 a wani harin ta’addanci a Makarantar Dakarun Soji na Musamman da ke Jihar Yobe a arewa maso gabashin ƙasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DCP Anthony Okon Placid, ya fitar ranar Asabar ta ce an kashe jami’an ne ranar 8 ga watan Mayu.
“Rundunar ‘yansandan Nijeriya tana baƙin cikin sanar da kashe jami’anta 17 yayin da suke aikin bautawa ƙasa sakamakon harin ta’addanci a Makarantar Dakarun Soji na Musamman da ke Buni Yadi a Ƙaramar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe da sanyin safiyar 8 ga Mayun 2026,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa ‘yansandan, waɗanda suke je makarantar domin samun horo na musamman, sun rasa rayukansu ne lokacin da ‘yanta’adda suka kai jerin hare-hare a makarantar.
Sanarwar ta ce: “Kazalika jajirtattun dakarun sojin Njeriya da dama sun rasa rayukan a yayin da suke daƙile harin.”
Babban Sufeton ‘yansandan Nijeriya Olatunji Disu ya bayyana ‘yansandan da aka kashe a matsayin waɗanda suke da “ƙarfin gwiwa da sadaukarwa” da nuna kishin ƙasa a yayin da suka halarci horo kan yaƙi da ta’addanci da wanzar da tsaro.
Ya miƙa saƙon ta’aziyyar ɗaukacin rundunar ‘yansandan Nijeriya ga iyalan jami’an da aka kashe tare da tabbatar musu cewa “ba za a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.”









