| Hausa
KASUWANCI
2 minti karatu
China za ta soke karɓar harajin fitar da kayayyaki daga ƙasashen Afirka 53
China ta ce daga 1 ga watan Mayu, ƙasar Eswatini ce kaɗai a cikin ƙasashen Afirka za ta ci gaba da biyan harajin kwastam a kan kayayyaki sakamakon har yanzu ƙasar na ci gaba da dangantaka ta diflomasiyya da Taiwan.
China za ta soke karɓar harajin fitar da kayayyaki daga ƙasashen Afirka 53
Shugaban kasar China, Xi Jinping. / Reuters
14 Fabrairu 2026

Shugaban kasar China, Xi Jinping, a ranar Asabar ya ce daga 1 ga watan Mayu, za a soke duk wani harajin fitar da kayayyaki zuwa duka ƙasashen, banda ƙasa ɗaya, kamar yadda kafafen watsa labarai na ƙasar suka ruwaito.

Dama tuni China ta soke kaɓar harajin ko sisin kwabo daga ƙasashen Afirka 33, inda a bara ta sanar da cewa za ta ƙara faɗaɗa tsarin zuwa ƙasashe 53 na Afirka.

China ita ce babbar abokiyar kasuwanci ta Afirka kuma babbar mai gudanar da ayyukan ababen more rayuwa a nahiyar ta hanyar shirin 'Belt and Road'.

Daga 1 ga Mayu, ba za a karɓi harajin kwastam ba daga dukkan kasashen Afirka sai Eswatini, wadda ke ci gaba da dangantaka ta diflomasiyya da Taiwan.

China na ikirarin tsibirin a matsayin mallakinta inda ta ce akwai yiwuwar za ta iya amfani har da ƙarfi domin ƙwace iko da shi.

Yawancin ƙasashen Afirka suna kara duba komawa hulɗa da China da sauran abokan kasuwanci tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba manyan haraji a duk duniya a bara.

Xi ya ce yarjejeniyar ba shakka za ta samar da sabbin damammaki ga ci gaban Afirka, inda yake sanar da ranar da za a cire wannan haraji a daidai lokacin da shugabannin na Afirka ke taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka a Ethiopia.

Rumbun Labarai
Naɗin 'ya'yan Dangote mata uku a manyan muƙamai: Sabon babi a tsarin gado na kasuwancin iyali
Me ya sa farashin zinare ke tashi a lokacin rikicin siyasa a duniya?
Gwamnatocin Afirka sun juya ga tsarin Bankin Musulunci bayan nasarar Sukuk a Benin
Ana sa ran kasuwanci tsakanin Turkiyya da Nijeriya ya kai dala biliyan 10 saboda sabbin yarjeniyoyi
Afrika na amfani da tagomashin da zinari yake samu don ƙara ƙarfin arziƙinta
Ghana ta biya basussukan dala biliyan 1.47 na fannin makashi da ake bin ta
Trump ya ce Amurka za ta karɓi gangar ɗanyen mai miliyan 50 daga Venezuela
Kamfanin Dangote ya yi watsi da ikirarin rufe matatar mansa
Me ya sa hanyoyin teku da aka toshe ke tayar da kura a Gabashin Afirka?
ECOWAS za ta cire harajin tafiye-tafiyen jiragen sama tsakanin ƙasashen Yammacin Afrika a 2026
Manyan ƙere-ƙeren fasaha na Afirka da suka yi tasiri a duniya
Abu biyar da ya kamata ku sani kan Taron G20 na farko a Afirka
An cire Nijeriya daga jerin kasashen da ake sa wa ido kan safarar kudade ba bisa ka'ida ba a duniya
Bai kamata kasuwanci da Afirka ya zama buƙatar ɗiban ma’adanai ba: Ministan Nijeriya Tuggar
Jamhuriyar Nijar ta kafa cibiyar tsaron intanet
Kamfanin simintin Dangote ya fara aiki a ƙasar Ivory Coast
Ana hasashen mambobin OPEC+ za su ƙara yawan fetur ɗin da suke fitarwa yayin da farashinsa ke karewa
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto