Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, ya sha alwashin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 bayan an naɗa shi Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya yi wannan alƙawarin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar yayin da yake gode wa Tinubu da jam’iyyar bisa yarda da suka yi da shi.
Yari ya ce shi ya karɓi wannan nauyi da “matuƙar godiya ” da kuma “cikakken muhimmanci”.
“Ina miƙa godiyata ta gaskiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar bisa amana da suka ba ni, da kuma shugabannin jam’iyyar bisa yarda da suka yi da ni. Ban ɗauke shi da wasa ba,” in ji shi he said.
Ya bayyana yaƙin neman zaɓen a matsayin abin da ya fi zaɓe, yana mai cewa zai ƙunshi tattaunawa da ‘yan Nijeriya a faɗin ƙasar game da makomar ƙasar.
“Yaƙin neman zaɓe ya fi zaɓe ɗaya kawai. Tattaunawa ce da ‘yan Nijeriya a ko wace jiha da ko wane yare da ko wane addini game da makomar da muke inawa tare,” a cewar Yari.
“Muna so mu jagoranci tattaunawar da kamun kai da haɗin kai da kuma mutunta kowa.”
Yari ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar APC da magoya bayanta a faɗin ƙasar su shiga yaƙin neman zaɓen.
“Da ɗaukacin mambobinmu da magoya bayanmu a faɗin ƙasar: aikin ya fara a yanzu, kuma kowa na da rawar da zai taka a cikinsa,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya daga dukkan jam’iyyu su goyi bayan sake zaɓan Shugaba Tinubu.
“Kuma ga dukkan ‘yan Nijeriya a ko wane ɓngare na siyasa, wannan shi ne wani lokaci na zaɓan ci-gaba maimakon rarrabuwan kawuna. Za mu samu yardarku ba da surutu kawai ba, amma da tarihin ayyukan da za mu iya nunawa,” in ji shi.
“Da yardar Allah, da kuma ƙoƙarin dukkanmu, za mu samar da nasara a watan Janairun 2027.”
Ranar Asabar ne dai jam’iyyar APC ta bayyana sunayen mutum 108 da za su jagoranci yaƙin neman zaɓen Shugaban Tinubu inda aka ayyana Abdulaziz Yari a matsayin Darakta Janar yayin da Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma zai kasance Sakataren Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen.
Kazalika jam’iyyar ta ayyana Shugaba Tinubu a matsayin shugaban majalisar yayin da Mataimakin Shugabanƙasa Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Nentawe Yilwatda, za su kasance mataimakan shugaban majalisar.





















