Majalisar Dokokin Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis
Za a gabatar da kwamitoci biyu na shaidu, ciki har da manyan jami'an Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da shugabannin addinai na Nijeriya.
Kwamitin Majalisar Wakilai ta Amurka kan Afirka ya sanya ranar Alhamis, 20 ga Nuwamban 2025, a matsayin ranar da za a fara bincike kan sake fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashin a Nijeriya.
Gayyatar da aka yi wa mambobin Kwamitin Harkokin Waje, wanda Channels Television ya rawaito cewa ya gani, an shirya za a yi ta ne da ƙarfe 11:00 na safe a Ɗaki mai lamba 2172 na Ginin Ofishin Gidan Rayburn, sannan kuma za a iya samun kallo ta intanet kai-tsaye, wanda wakili Chris Smith (R-NJ) ne zai jagoranta.
Za a gabatar da kwamitoci biyu na shaidu, ciki har da manyan jami'an Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da shugabannin addinai na Nijeriya.
Gayyatar tana cewa, "Ana roƙonku da girmamawa da ku halarci zaman sauraron ƙararraki na Kwamitin Harkokin Waje da ƙaramin kwamiti kan Afirka zai gudanar da shi da ƙarfe 11:00 na safe a ɗaki mai lamba 2172 na ginin Ofishin Rayburn House."
Trump ne ya fara sanya Nijeriya a matsayin kasae da ake sa wa ido na musamman, CPC a shekarar 2020, kafin magajinsa, Shugaba Joe Biden, ya cire ƙasar daga jerin sunayen bayan ya kayar da Trump.
Masu sauraron za su haɗa da Babban Jami'in Ofishin Harkokin Afirka, Jonathan Pratt, da Mataimakin Mataimakin Sakatare na Ofishin Dimokuradiyya, 'Yancin Dan’Adam, da Aiki, Jacob McGee.
Za a yi zaman tattaunawa ta biyu da Daraktan Cibiyar 'Yancin Addini, Ms Nina Shea; Bishop Wilfred Anagbe na Makurdi Catholic Diocese a Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya.
Ana sa ran zaman tattaunawa ta majalisar zai sake duba girman zargin cuzguna wa masu wani addini a Nijeriya.
Za a kuma yi nazarin irin martanin manufofi da za a iya ɗauka, ciki har da takunkumin da aka yi niyyar ƙaƙabawa da taimakon jinƙai, da haɗin gwiwa da hukumomin Nijeriya don hana ƙarin tashin hankali.
Za a kuma gabatar da kudirin a gaban Majalisar Dattawan Amurka, wanda Sanata Ted Cruz ya ɗauki nauyinsa.