| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yanbindiga a Kano tare da ƙwato kudin fansa
Dakarun Sojojin Nijeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi, tare da kwato kuɗin fansa naira miliyan 10 a wani samame da suka gudanar a dajin Falgore.
Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yanbindiga a Kano tare da ƙwato kudin fansa
Dakarun Briged ta 3 ne suka gudanar da samamen ƙarƙashin shirin Operation MESA, bayan sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Fanyabo

Dakarun Sojojin Nijeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi, tare da kwato kuɗin fansa naira miliyan 10 a wani samame da suka gudanar a dajin Falgore, Ƙaramar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano.

Dakarun Briged ta 3 ne suka gudanar da samamen ƙarƙashin shirin Operation MESA, bayan sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Fanyabo da ke cikin dajin Falgore a ranar 11 ga Oktoba, 2026.

A cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji na Birged ta 3, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Asabar, ya ce an yi garkuwa da mutumin ne yayin da yake dawowa daga kasuwar Yandoka da ke Jihar Kaduna da tsakar dare.

Sanarwar ta ce daga bisani masu garkuwar sun tuntubi iyalan wanda aka sace a ƙauyen Yan Taburmi, wanda shi ma yake cikin dajin Falgore, inda suka nemi a biya kuɗin fansa domin sakin sa.

A cewar rundunar sojin, dakarunta sun yi aiki bisa sahihan bayanan sirri, inda suka shirya kwanton-ɓauna tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da mafarautan yankin.

Sanarwar ta ce: “Samamen ya yi sanadin kashe mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da samun nasarar kuɓutar da wanda aka sace, yayin da sauran mambobin ƙungiyar masu garkuwar suka tsere zuwa cikin dajin Falgore.”

Ta ƙara da cewa wani bincike da aka gudanar a yankin bayan samamen ya kai ga gano naira miliyan 10 da aka ce iyalan wanda aka sace sun biya a matsayin kuɗin fansa.

Sanarwar ta bayyana cewa an mayar da kuɗin da aka kwato ga wanda aka yi garkuwa da shi da iyalansa.