| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Ƙarin ma'aikatan jinya sun shiga yajin aiki yayin da cutar Ebola ta kama kusan mutum 3,000
Adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Kongo ya kai 2,973, ciki har da mutum 1,309 da suka mutu, in ji ƙididdigar da gwamnati ta fitar ranar Jumma’a a batun da hukumomi suka tabbatar cewa shi ne yaɗuwar cutar da ta fi sauri a tarihi.
Ƙarin ma'aikatan jinya sun shiga yajin aiki yayin da cutar Ebola ta kama kusan mutum 3,000
Ma'aikatan jinya na zanga-zanga a gaban cibiyar kula da masu cutar Ebola ta Elikya a Bunia, Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, ranar 25 ga Yulin 2026.

Ma’aikatan jinya a wata cibiyar kula da masu cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun tsunduma cikin yajin aiki ranar Asabar bisa batun biyansu, lamarin da ya katse kulawa da masu jinya a tsakiyar inda cutar ta fi ƙamari a ƙasar inda annobar ke ƙaruwa cikin sauri.

Ma’aikatan da adadinsu ya kusan 100 sun ce rashin biyansu alawus-alawus na zagon ƙasa ga ƙwarin gwiwarsu da kuma katse kula da majiyanta.

Adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Kongo ya kai 2,973, ciki har da mutum 1,309 da suka mutu, in ji ƙididdigar da gwamnati ta fitar ranar Jumma’a a batun da hukumomi suka tabbatar da cewa shi ne yaɗuwar cutar da ta fi sauri a tarihi.

Yawancin harkoki a cibiyar kula da masu cutar Ebola ta Elikya a Bunia, lardin Ituri, sun tsaya bayan likitoci da ma’aikatan jinya da masu gadi suka daina aiki.

Kimanin ma’aikatan jinya 100 sun yi zanga-zanga a wajen cibiyar jinyar ranar Asabar. Sun ce alawus-alawus ɗin da ba a biya ba suna rage ƙwarin gwiwar ma’aikata da kuma katse kula da majinyata, kuma sun yi kira ga hukumomin ƙasar Kongo su biya kuɗaɗen da suke bin hukuma domin su koma bakin aikinsu.

‘Kuɗaɗen ladan aikin da ba a biya ba’

A cikin wata sanarwar da suka fitar ranar Jumma’a, ma’aikatan dukkansu sun haɗa baki wajen amincewa da fara yajin aikin daga ranar Asabar har zuwa lokacin da aka samu “mafita ƙwaƙƙwara” domin magance matsalar “wata biyu na rashin biyan kuɗaɗen ladan aiki.”

A makon da ya gabata, ma’aikatan jinya a babban asibitin Bunia, cibiyar lafiya mafi girma a yankin, sun tsunduma cikin yajin aiki sakamakon rashin biyan albashi. Wasu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AP cewa ba a biya su komai ba tun da suka fara aiki a lokacin da annobar ta ɓarke.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce fiye da ma’aikatan jinya 100 ne suka kamu da cuta tun ɓarkewar annobar.

Ƙasar ta tsakiyar Afirka tana fama da ɓarkewar annobar wadda ƙwayar cutar Bundibugyo da ba saba gani ba ce haddasa ta tun ranar 15 ga watan Mayu. Majinyata 766 suna keɓe ko kuma a cikin asibitoci, yayin da 540 suka warke kawo yanzu, in ji alƙalluman da ma’aikatar Lafiyar Kongo ta fitar.

Bazuwa fiye da matakai

Lardin gabashi na Ituri ne ke da kusan kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar.

Annobar ta ci gbada da yaɗuwa fiye da iya yadda ma’aikatan jinya ke iya bibiyarta duk da cewa suna faɗaɗa matakan da suke ɗaukawa a kanta.

Giɓin kuɗi da hare-hare kan cibiyoyin lafiya da yaƙin da ke yi a gabshin Kongo da rashin yarda tsakanin al’ummomin yankin ne ke tarnaƙi ga matakan da ake ɗaukawa kan annobar.