Yaya kaifin basira da fahimtar tausayi yake tsakanin giwaye?

Masu bincike da masu nazarin namun daji sun lura da halayyar da ke nuna giwaye suna iya nuna damuwa, kuma suna da tsarin dangantaka mai sarƙaƙiya. A yanayi da yawa, rayuwarsu ta fahimtar zuci tana kama da tamu ta mutane.

By
HOTON TARIHI: Wani dan giwar Asiya yana samun taimako daga mahaifiyarsa Farina don ya tashi tsaye a gidan namun daji na Pairi Daiza da ke Brugelette. / Reuters

Giwaye suna yawan burgewa saboda girman jikinsu da ƙasaitarsu. Amma baya ga wannan kwarjinin nasu a ido, akwai wani abu mafi ban mamaki game da su: abin da ke ɓoye a zuciyoyinsu na kaifin tunani.

Masu nazari sun daɗe suna rubutu kan halayyarsu da ke nuna cewa giwaye na da tausayi, da tsarin dangantaka mai sarƙaƙiya, da kuma iya nuna juyayi. A hanyoyi da dama, rayuwarsu ta zuci tana kama da tamu ta mutane.

To, yaya kaifin basira da fahimtar tausayi yake tsakanin giwaye?

Halittu masu nuna damuwa

Ana yawan ɗaukar giwaye a matsayin halittu waɗanda suka fi iya nuna damuwa.

A cikin daji, jariran giwa suna dogaro sosai kan uwayensu da sauran dangi don tsira a shekarun farko na rayuwarsu. Masu bincike na ƙungiyar World Animal Protection sun lura cewa a shekaru huɗu zuwa biyar na farkon rayuwa, yara ‘ya’yan giwa suna koyon muhimman ƙwarewa kamar yadda za su ci, sadarwa, da kuma halayen zamantakewa daga garke.

Giwaye mata yawanci suna zama cikin garke iya tsawon rayuwarsu, inda suke kafa tsarin jagorancin ƙungiyoyi wanda mata ke shugabanci. Giwaye maza, a gefe guda, sau da yawa suna barin garken a lokacin balaga.

Jariran giwa ba sa yawan nisa daga 'yan’uwansu. Masu bincike sun nuna cewa jariran giwa na Afirka suna kashe kusan “kashi 90 cikin 100 na lokacinsu cikin nisan mita 5 daga wata giwar”, abin da ke nuna muhimmancin kusantar jiki da tallafin zamantakewa.

Baƙin ciki da makoki

Wataƙila hujjar da ta fi ƙarfi game da tausayin giwaye tana bayyana ne a yadda suke martani kan mutuwa.

Giwaye suna cikin ɗan ƙaramin rukunin nau’o’in dabbobi waɗanda ake ganin su suna nuna alamun baƙin ciki. An gan su suna dawowa sau da yawa wurin gawar wasu 'yan’uwansu, suna taɓa ƙashi da hancinsu, sannan kuma suna tsayawa shiru kusa da gawar har na dogon lokaci.

Masu aikin kare muhalli sun ce jariran giwa na musamman kan nuna matuƙar jin raɗaɗin rasa ’yan’uwa. Idan jariri ya rasa mahaifiyarsa kafin ya kai shekaru biyu, yiwuwar tsiran rayuwarsa za ta ragu sosai, cewar World Animal Protection.

Kare marasa ƙarfi

Ana kuma ganin giwaye suna da iya hango haɗari da shiga tsakani don kare 'yan garken da suka fi rauni ko ƙarancin shekaru.

Masu bincike sun yi rubutu kan lokuta da manyan giwaye, mata iyaye da kuma wasu mata da ba su da alaƙar, sukan tsaya tsayin daka don kare jariran daga barazanar da za ta iya tasowa. Suna iya kore dabbobi mafarauta, tsayar da wasan da ya yi tsanani, ko kuma sanya kansu a tsakankanin jariran da haɗari.

Abin da ya sa wannan hali ya bayyana sosai shi ne cewa sau da yawa yana faruwa “kafin jariri ya nuna alamar tashin hankali”, in ji masu binciken.

Masana sun yi imanin cewa giwaye na iya yin amfani da abubuwan da suka faru a baya don hango yadda jariri zai ji a yanayin barazana. Ɗaukar mataki kafin a sami lahani na nuni da wani matakin fahimtar zuci, wanda ba a saba ganin irin sa a yawancin dabbobi ba.

Rayuwar zamantakewa mai sarƙaƙiya

Giwaye na rayuwa a wani tsarin da ke da sarƙaƙiyar cuɗanya mafi zurfin cigaba a duniyar dabbobi.

Giwayen Afirka suna kafa manyan garke masu sarƙaƙiyar dangantaka waɗanda za su iya haɗa giwa gommai, har zuwa ɗaruruwa. Giwayen Asiya, waɗanda a da ake tunanin suna rayuwar kaɗaici, su ma suna da hanyoyin zamantakewa mai sarƙaƙiyar cuɗanya, ko da yake dangantakarsu tana iya faɗaɗuwa zuwa nesa.

Giwayen Asiya mata suna iya samun 'abokan zumunci' daga 10 zuwa 50, suna sadarwa tsakaninsu ta hanyar ƙamshi da sauti mara ƙara wanda ke iya tafiyar kilomita da dama a cikin fili.

Waɗannan isharori suna ba wa giwaye damar sanin motsin junansu, ko da suna nisan mil guda tsakaninsu.

Haka nan giwaye na daga cikin tsirarun dabbobin da za su iya gane kansu a madubi.

A gwaje‑gwajen kimiyya, ana sanya alama a jikin dabba a wurin da za ta iya gani kawai ta madubi. Idan dabba ta yi amfani da madubi don duba alamar a jikinta, hakan na nuni da wani matakin sanin-kai.

Giwayen Asiya sun ci wannan gwajin, wanda ya sanya su cikin rukuni guda da manyan birrai da kuma kifin dolphin.

Ƙungiyar World Animal Protection ta lura cewa yara ‘ya’yan bil-adama yawanci suna samun wannan fahimta ne kaɗai tsakanin watanni 18 zuwa 24 da haihuwa.

Giwaye kuma ƙwararru ne wajen warware matsaloli.

A cikin daji, suna amfani da rassan itace don kore ƙwari, har an ma taɓa ganin su suna rufe gawarwaki da ciyawa. Ikon su na sarrafa abubuwa na nuna kaifin basirar ƙirƙira da kuma sanin muhalli.

A wani misali mai jan hankali, masu gadin daji sun ruwaito cewa giwaye sun toshe wata hanya da aka gina don wani aiki rage yawan dabbobi, ta hanyar jawo rassan itace suna rufe hanyar gabaɗaya.

Tuna abubuwa tsawon rayuwa

Akwai wata tsohuwar karin magana mai cewa, “giwa ba ta mantuwa”, kuma wataƙila maganar ta dace da gaskiya.

Nazarin ya nuna cewa giwaye na iya tuna wasu abubuwa na musamman da aka danganta da lada ko sakamako, har ma bayan shekaru takwas. Giwayen Afirka na iya gane kiran mambobin iyali da suka bar garke “sama da shekaru goma da suka wuce”, in ji World Animal Protection.

Waɗannan ƙarfin ƙwaƙwalwa na da muhimmanci wurin tsira, kuma yana taimaka musu wajen samun abinci da wurin shan ruwa da kuma kula da dangantakar zamantakewa a faɗin wuri mai nisa.

Amma irin wannan hankali da zurfin fahimtar zuci yakan zo da nasa raunin.

Giwaye da suka fuskanci firgici mai wahala, kamar ganin ‘yan uwansu ana kashe su ta hannun ɓarayi mafarauta, suna iya nuna alamun damuwar tunani. A matsugunan marayu da ke kula da jariran giwa da aka ceto, an ga wasu daga cikin yara suna farkawa cikin dare suna kuka da ihun tsoro bayan yanayin da suka shiga.

Halayensu na nuna cewa, kamar mutane, giwaye na iya maimaita tunanin azaba har bayan lokacin da abin ya faru.

Ilminn zamuna

Garken giwaye yakan ginu da tunanin yaɗa ilimi tsakanin mambobin garke daga zamani zuwa zamani.

Mata masu shekaru, musamman uwar garke, suna da muhimmiyar rawa wajen jagorantar garke. Ƙwarewarsu na taimakawa matasan giwaye wajen tsallake haɗari, gano abinci da ruwa, da kuma tsira a mawuyacin yanayi.

Masu lura sun gano misali cewa, mata manya wani lokacin sukan fara ƙetare hanyoyi masu cunkoso da farko, don tabbatar da tsaro kafin su bar jarirai su bi. Sannan su jagoranci matasa su ƙetare hanyoyin kafin su bi su a baya.

Wannan hali yana nuna yadda giwaye ke da wata ɗabi’a mai zurfi ta kare mambobin garke da ke da rauni.

Masana har yanzu na ci gaba da gano sabbin bayanai game da hankalin giwaye, da rayuwar zuciyarsu. Amma abin da ya riga ya bayyana shi ne waɗannan dabbobi sun fi kaifin basira a zamantakewa fiye da yadda aka taɓa zato.

Wannan yana sa kariya ga giwaye ta zama abin gaggawa.

Ana ci gaba da zaluntar su a harkar yawon buɗe-ido, da lalata muhallinsu, kuma farautar haram na ci gaba da barazana ga yawan giwaye a Afirka da Asiya. Kare su ba wai batun kare wani nau'in halitta ba ne kawai, amma yana tabbatar da lafiyar ɗaya daga cikin halittu mafi ban mamaki a duniyar dabbobi.