Fararen-hula fiye da 1,600 sun tsere daga yankin Kordofan na Sudan a kwana ɗaya, in ji Hukumar IOM

Sanarwar Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) na zuwa ne a yayin da rundunar sojin Sudan ta ce dakarunta sun sake ƙwace yankuna da dama a Abbasiya Tagali a Kudancin Kordofan bayan sun yi arangama da mayaƙan RSF

By
People prepare to travel about 250 km south to Adre, on the Chad-Sudan border, at a transport station in Tine / Reuters

Fiye da fararen hula 1,600 ‘yan Sudan ne suka tsere daga garin Kertala a South Kordofan a rana ɗaya yayin da tsaron ya taɓarɓare tare da ƙarin cinzarafi da rundunar Rapid Support Forces (RSF) ke yi, a cewar hukumar da ke kula da masu ƙaura ta Duniya (IOM) .

Hukumar ta Majalisar Ɗinkin DUniya (MDD) ta bayyana ranar Lahadi cewa wakilanta a ɓangaren da ke sa ido a kan waɗanda aka raba gidajensu a yankin sun yi ƙiyasin cewa mutum 1,625 sun bar Kertala ranar 28 ga watan Nuwamba saboda taɓarɓarewar yanayin tsaro da ke da alaƙa da ƙeta haƙƙi na RSF .

Hukumar ta ce mutane da aka raba da gidajensu sun bazu zuwa wuraren da ke Dalami, tana mai gargaɗin cewa yanayi a wurin na cike da rashin tabbas da zaman ɗardar.

Daga farko dai a ranar Lahadi, rundunar sojin Sudan ta ƙwace wasu wurare yamma da Abbasiya Tagali a South Kordofan bayan arangama da RSF da ƙawarta, ɓangaren SPLM-North , kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu Agency.

A ranakun Juma’a da Asabar, sojin ta daƙile wani harin RSF kan Kertala a jihar .

Guguwar raba mutane da gidajensu na baya-bayan nan na zuwa ne bayan hare-haren RSF – da taimakon ɓangaren SPLM-North – kan wasu ƙauyuka a South Kordofan, ciki har da garkuwa da matasa domin a tilsta musu zama mayaƙa.

Yanki mai cika da rashin tabbas

Jihohin Kordofan ukun– North, West and South – sun fuskanci makonni na yaƙi tsakanin soji da RSF, lamarin da ya sa gomman dubanni mutane suka tsere , in ji ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama.

Daga cikin jihohin Sudan 18, RSF na iko ne kan jihohi biyar na yankin Darfur a yammacin ƙasar , face wasu yankunan arewacin jihar North Darfur da ke a ƙarƙashin ikon soji kawo yanzu.

Ita kuwa sojin tana riƙe da da yawa daga cikin sauran jihohi 13 da suka saura a kudanci da arewaci da gabashi da kuma tsakiyar ƙasar ciki har da babban birnin ƙasar, Khartoum.

Rikici tsakanin sojin Sudan da RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya kashe aƙalla mutum 40,000 tare da raba mutum miliyan 12 da gidajensu, in ji hukumar lafiya ta duniya WHO.