Nijeriya ta dakatar da aiwatar da harajin kashi 15% kan shigar da fetur da dizal cikin ƙasar
Tun farko manufar wannan matakin ita ce ƙarfafa masana’antun tace man cikin gida kamar su Matatar Dangote da ƙananan masana’antun tace mai, ta hanyar sanya man da ake shigar da shi daga waje ya fi tsada.
Hukumar kula da harkokin sarrafawa, tacewa da sufurin man fetur ta Nijeriya, NMDPRA a ranar Alhamis ta bayyana cewa ta jingine aniyarta ta aiwatar da harajin kashi 15 cikin ɗari da aka tsara a kan shigar da man fetur daga waje zuwa cikin ƙasar.
Daraktan Sashen Harkokin Jama’a na NMDPRA, George Ene-Ita ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya yi gargadin jama’a da su guji sayen man da gaggawa saboda tsoron ƙarewa.
A ranar 29 ga Oktoba, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da saka harajin shigo da man fetur da dizal — wata manufa da ake sa ran za ta ƙara farashin shigo da man daga ƙasashen waje.
Tun farko manufar wannan matakin ita ce ƙarfafa masana’antun tace man cikin gida kamar su Matatar Dangote da ƙananan masana’antun tace mai, ta hanyar sanya man da ake shigar da shi daga waje ya fi tsada. An tsara fara aiwatar da wannan manufa ne a ranar 21 ga Nuwamban 2025.
Sai dai a wani sabon bayani, NMDPRA ta ce gwamnati ta daina la’akari da ci gaba da aiwatar da harajin shigo da man fetur.
“Ya kamata a lura cewa aiwatar da harajin kashi 15 cikin ɗari a kan shigo da Man Fetur da Diesel ba ya cikin shirin gwamnati a yanzu,” in ji wani ɓangare na sanarwar.
A cikin sanarwar, hukumar ta NMDPRA ta tabbatar wa jama’a cewa akwai wadataccen man fetur a ƙasar a matakin da aka amince a daidai wannan lokacin da ake matuƙar buƙatar fetur ɗin.
Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu son ɓoye man fetur ɗin da masu rige-rigen sayen fetur ɗin domin farbagar ƙarewa kan cewa akwai wadataccen man a ƙasar.