'Yansanda a Jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya sun ce mutane 20 ne suka mutu a wani hari da aka kai karshen mako kan wata al'umma a karamar hukumar Bokkos.
Wannan shi ne sabon hari a jerin hare-haren rikicin kabilanci da na al'umma da suka addabi yankin duk da yawan tura jami'an tsaro da alkawuran gwamnati na kawo karshen tashe-tashen hankula.
Jihar Filato na daga cikin jihohin da ke yankin Tsakiyar Nijeriya (Middle Belt), wanda ya kunshi kabilu da addinai daban-daban, inda rikice-rikicen al'umma suka yi sanadin asarar daruruwan rayuka cikin 'yan shekarun nan.
Kakakin rundunar 'yansandan Jihar Filato, Alfred Alabo ya ce jami'an tsaro tare da sauran hukumomin tsaro sun yi musayar wuta mai tsanani da maharan da sanyin safiyar Lahadi kafin daga bisani maharan suka tsere.
An tura karin jami'an tsaro
Alabo ya ce mutum 18 sun mutu a wurin harin, yayin da wasu biyu suka rasu daga baya a asibiti.
Ya kara da cewa Kwamishinan 'Yansandan Jihar Filato, Bassey Ewah, ya ba da umarnin tura karin jami'an tsaro yankin, ciki har da jami'an rundunonin musamman da na sintiri.
Rahoton tsaro da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya gani ya nuna cewa dakarun rundunar Operation Enduring Peace sun amsa kiran gaggawa tare da gano gawarwaki 12 a kauyen Kawel da wasu shida a kauyen Kopkon.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Alfred Alabo, ya ce ana ci gaba da kokarin dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Tarihin hare-hare
A makonnin baya-bayan nan, Jihar Filato ta sake fuskantar karuwar hare-hare masu janyo asarar rayuka.
A ranar 15 ga Yuni, akalla mutum takwas sun mutu yayin da sama da mutum 10 suka jikkata bayan wasu 'yanbindiga sun kai hari kauyen Gwon-Ajang da ke karamar hukumar Barkin Ladi a lokacin wani bikin ranar haihuwa.
A farkon wannan watan kuma, mutum uku sun mutu a hare-hare daban-daban a karamar hukumar Riyom, yayin da wasu bakwai, ciki har da wani sufeton 'yan sanda, suka mutu a hare-haren da aka kai a wasu al'ummomi a Barkin Ladi.
Wadannan hare-haren sun sa Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, sanar da karin matakan tsaro, ciki har da takaita kiwon dare da ayyukan hakar ma'adanai a yankunan da ke cikin hadari.
Takaddama kan filaye da albarkatu, rikice-rikicen al'umma da kuma sabanin da ke tsakanin manoma da makiyaya na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a Jihar Filato, daya daga cikin yankunan da suka fi fama da tashe-tashen hankali a Nijeriya.
















