Ministan Turkiyya Fidan na yin tuntubar diflomasiyya a tsaka da hare-haren Amurka da Isra’ila a Iran

Hakan Fidan ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa da suka hada da na Iran, Qatar, Saudiyya, UAE, Faransa, Spaniya da Jordan inda suke neman a tsahirta kai hare-hare.

By
Fidan ya tattauna da ministocin harkokin wajen yankin don neman mafitar dakatar da rikicin. / AA / AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gudanar da tattaunawa mai zurfi a cikin kwanaki uku da suka gabata ta hanyar kiran waya a yayin da ake tsaka da fuskantar hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran da kuma matakan martani daga Tehran, in ji majiyoyi.

Bayan harin hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, Fidan ya yi magana da ministocin harkokin waje na Iran, Iraki, Saudiyya, Qatar, Siriya, Masar da Indonesia don tattauna ci gaba da kuma matakan da za a dauka don dakatar da hare-haren.

A wannan rana dai, ya kuma tattauna ta wayar tarho daban-daban da takwarorinsa na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Spaniya da Hungary don neman hanyoyin magance hare-haren yankin.

A wani kiran wayar tarho da ya yi da shugaban saita manufofin harkokin waje na Tarayyar Turai Kaja Kallas, Fidan ya kimanta karuwar da ake samu a yankin. Su biyun sun tattauna kan shirye-shiryen diflomasiyya da ake ci gaba da yi da nufin dakatar da rikicin.

A ranar Lahadi, Fidan ya yi musayar ra'ayoyi da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi kan sabon yanayin da ake ciki a Iran. Ya kuma yi magana da Ministan Harkokin Wajen Oman Badr Albusaidi duk da manufar magance rikicin yankin.

A ranar Litinin, ministan ya yi kira wayar Ministan Harkokin Wajen Azerbaijan Jeyhun Bayramov don tattauna kokarin kawo karshen rikici a yankin. Ya kuma yi magana da Ministan Harkokin Wajen Bulgaria Nadezhda Neynsky, inda suka yi tsokaci kan tasirin rikici a yankin.

Daga baya, a cikin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noel Barrot, Fidan ya tabo batun cigaban yankin dalla-dalla. Tattaunawar ta hada da musayar matakai na zahiri don rage tashin hankali da kawo karshen hare-haren.

Fidan ya kuma tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Jordan Ayman Safadi. Tattaunawar ta shafi fannoni na siyasa, tsaro da jinkai na baya-bayan nan a yankin, tare da mai da hankali kan kawo karshen hare-haren, rage tashin hankali da kuma karfafa kokarin diflomasiyya tare da masu ruwa da tsaki.