Gobara ta ƙona shaguna aƙalla 50 a Kasuwar Fatima Simra a Kanon Nijeriya

Shugaban kwamitin kashe gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula ya ce gobarar ta lalata shaguna fiye da 50 yayin da wutar ke ci gaba da ci zuwa lokacin.

By
Iftila'in gobara ya lakume shaguna akalla 50 a kasuwar Fatima Simra da ke jihar Kano a Nijeriya / Others

Wani sabon iftila’in gobara ya ƙona shaguna akalla 50 a Kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose Market da ke cikin babbar Kasuwar Dakata a Jihar Kano da ke yankin arewacin Nijeriya.

Gobarar ta ɓarke ne da sanyin safiyar Jumma’a, tsakanin ƙarfe 5:30 zuwa 6:00 na safe, kuma ta bazu cikin sauri inda ta ƙona shaguna da dama, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Yawancin shagunan da abin ya shafa na ƙananan ‘yan kasuwa ne waɗanda ke sayar da mai da kuma robobi da sauransu.

Jami'in Hulɗa da Jama'a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana cewa zuwa yanzu, ‘‘jami’an kashe gobara suna koƙarin shawo kan wutar.’’

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a tantance cikakken adadin ɓarnar ba da gobarar ta haifar ba, “za a fara bincike tare da tantancewa bayan an kashe gobarar gaba ɗaya’’ in ji shi.

Shugaban kwamitin kashe gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, shi ma ya tabbatar da lamarin, yana cewa ‘‘tuni gobarar ta ƙone shaguna kusan 50.”

Ya ce an yi ƙoƙarin sanar da hukumar kashe gobara da sauran hukumomin da abin ya shafa, wadanda suka riga suka iso wurin.

Lamarin ya faru ne kasa da mako guda bayan wata mummunar gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke jihar Kano wadda ta gona shaguna fiye da 1,000, lamarin da ya haifar da fargaba game da tsaron gobara a manyan kasuwannin jihar mafi yawan jama’a a arewacin Nijeriya.