Yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewa tauraron ɗanwasan Barcelona, Raphinha, zai bar ƙungiyar, ɗanwasan ya mayar da martani kan jaridun Sifaniya da ke yawan tattauna batun.
A wata hira da shafin ESPN, ɗanwasan ɗan asalin Brazil ya yi watsi da hasashen barin Barca, yana mai cewa rahotannin da ke nuna shakkunsa kan zamanasa a Barca ƙarairayi ne kawai.
Raphinha ya ce, “Akwai wani ƙato da ba shi da aiki sai ƙarya… Tun da na zo Barcelona ake ta hasashe kan tafiyata daga kulob ɗin tun ran farko da na zo”.
Ɗanwasan mai shekaru 29 bai ambaci wanda yake nufi ba, amma dai a fili yake cewa yana magana ne kan rahotannin da ake yaɗawa wanda suka ɓata masa rai.
Raphinha yana da kwantiragi da Barcelona da za ta kai har 2028, wanda ke nufin ba ya buƙatar tattaunawa kan batun tsawaita zamansa ba.
Tun zuwansa Barca, ɗanwasan ya nuna hazaƙa sosai amma yana yawan samun rauni da ke kai shi jinya. Ya ci ƙwallo 19 da tallafin ƙwallo takwas a wasanni 31.
Rabon Raphinha da buga wa Barcelona wasa tun watan Maris, sakamakon rauni a cinyarsa. Amma an gan shi a benci a wasan da Barca ta doke Osasuna da ci 2-1, ranar 2 ga Mayu.
Ana sa ran zai buga wasan El Clasico da Real Madrid, a wasan da ake ganin daga shi ne Barca za ta ɗaga kofin La Liga na bana.












