Rundunar ‘yansandan Afirka Ta Kudu ta bayyana a ranar Talata cewa mutuwar wani mutum ɗan Nijeriya a hannunta a ƙarshen watan da ya gabata ba ta da wata alaƙa da ƙarin aukuwar tashin hankali kan kyamar baƙi, tana mai cewa mutumin ya faɗi ne bayan an kama shi da miyagun ƙwayoyi.
Ministar Harkokin Wajen Nijeriya ta yi zargi ranar Lahadi cewa mutumin ya mutu ne a lokacin da ‘yansandan Afirka Ta Kudu ke masa tambayoyi kwanaki biyu gabanin gangamin da aka yi a faɗin ƙasar game da ƙyamar baƙin-haure, tana mai barazanar ɗaukar matakin da ba ta bayyana ba idan aka samu ƙarin hare-hare kan ‘yan ƙasar.
"Hukumar ‘yansandan Afirka ta Kudu ta yi watsi da ƙoƙarin alaƙanta wannan lamarin da jerin zanga-zangar ƙin baƙin-haure," kamar yadda wani mai magana da yawun ‘yansanda ya bayyana a wata sanarwa.
Mai magana da yawun rundunar ya ce wata tawagar ‘yansanda da ke bincike kan miyagun ƙwayoyi ta kama wani ɗan Nijeriya a gidansa a wani samame bisa bayanan sirri.
An samu miyagun ƙwayoyi a wurin, kuma mutumin ya faɗi ne a lokacin da ake tafiya da shi wani ofishin ‘yansanda na Pretoria, kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyana.
An kira ma’aikatan jinya, kuma sun tabbatar da cewa ya mutu, yayin da aka sanar da wata hukuma mai sa ido kan aikin ‘yansanda, kuma za ta yi bincike kan lamarin, kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya bayyan.
Ma’aikatar harkokin wajen Afirka Ta Kudu ta nemi gwamnatin Nijeriya ta tura duk wata hujjar da take da ita game da mutuwar mutumin, amma ba ta yi magana game da zarge-zargen da takwararta ta Nijeriya ta yi ba.
Yawancin zanga-zangar ƙin baƙi a cikin ‘yan watannin da suka wuce sun kasance na lumana, amma a wasu lokuta sukan rikaɗa su zama na tashin hankali, inda ake kai hare-hare kan ‘yan ƙasashen waje, da kuma wawashe kayayyakin shagunan baƙi.
Ƙungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce ana ɗaura wa ‘yan ƙasashen waje laifin manyan matsaloli kamar aikata laifuka da rashin ayyukan yi.















