Me ya sa jaruman Nollywood Kate Henshaw da Genevieve Nnaji da Rita Dominic ba sa tsufa?
An ɗauki wannan hoton ne a shekarar 2011, amma a halin yanzu Kate Henshaw ta kai shekaru 54 da haihuwa / Reuters
Me ya sa jaruman Nollywood Kate Henshaw da Genevieve Nnaji da Rita Dominic ba sa tsufa?
Ma'abota kallon fina-finan suna ganina jaruman suna nan tamkar yadda suke sama da shekaru 20 da suka wuce ne inda ake yawan saka su a fina-finan nollywood.
21 Yuli 2025

‘Kimanin shekaru hamsin a duniya, amma tamkar budurwa!’ Wannan shi ne irin kalaman da mutane suke ta furtawa a shafukan sada zumunta kwanan nan game da hotunan da wasu jarumar masana’antar fina-finan Turanci na Nijeriya, Nollywood suke wallafawa a shafukansu.

Ma’abota kallon fina-finan suna ganin jaruman suna nan tamkar yadda suke sama da shekaru 20 da suka wuce ne inda ake yawan saka su a fina-finan Nollywood.

Dubban mabiya na sharhi

Kate Henshaw wadda ta cika shekara 54 a duniya na ɗaya daga cikin jaruman da mutane ke mamakin yadda take matashiya a ido duk da yawan shekarunta.

Kate na da mabiya miliyan 3.3 a shafinta na Instagram kuma tana da mabiya miliyan 1.2 a shafinta na X.

Ranar 19 ga watan Yuli ta wallafa hotuna a shafukanta na Instagram da na X domin bayyana murnarta da cika shekaru 54 a duniya.

A shafinta na Instagram mutum sama da 135,000 ne suka nuna suna son saƙon inda mutum sama 10,900 suka bayyana ra’ayoyinsu game da saƙon nata. 

A shafinta na X kuma saƙon ya samu ra’ayoyi sama da 3,000 inda mutum sama da 353,200 suka kalli hotunanan.

Ita kuwa Rita Dominic a cikin watan Yulin shekarar 2025 ne ta cika shekara 50 a duniya. A shafinta na Istagram tana da mabiya miliyan 7.6 yayin da mutum miliyan 1.3 ke bin ta a shafinta na X.

A saƙon da ta wallafa na murnar zagoyarwa ranar haihuwarta a shafinta na Instagram, Rita ta samu ra’ayoyi 9,656 kuma mutum fiye da 171,000 sun nuna suna son saƙon.

Saƙon da ya ƙunshi hoton bidiyon jarumar da jaruma Genevive Nnaji ya samu shiga shafin Genevive na X.

Bidiyon ya yi jan hankalin mutane a shafin Genevive na X inda kimanin mutumun 459,000 suka kalli bidiyon kuma mutum fiye 21,000 suka nuna suna son bidiyon.

“’Yan mata za su ci gaba da zama ‘yan mata a lokuta mara adadi,” in ji Genevive a saƙon taya Rita Dominic murnar cika shekara 50 da ta wallafa wa  shafinta na X.

Me ya sa suke kamata da ‘yan mata?

Waɗanda suka san Kate Henshaw dai sun ce ba ta wasa da motsa jiki. An tabbatar da cewa ba ta wasa da fita gudu da kuma zuwa ɗakin motsa jiki.

Wasu ‘yan Nijeriya da suka haura shekaru hamsin suna ta sha’awar kasancewa suna da irin jikin Kate, sai dai ba sa son jure irin wahalar da take sha wajen tabbatar da hakan.

Wannan na cikin abubuwan da ake ganin sauran jaruman ke yi domin tsawaita ƙuruciyarsu.

Baya ga haka ana ganin jaruman suna kula da ababen da suke ci da kuma yanayin yadda suke cin abincinsu domin tsawaita cigaba da tafiya da irin jjikin da aka san su da su tun a baya.

Bugu da ƙari ana ganin jaruman suna ƙula da lafiyarsu ta jiki da fatan jiki ba tare da shafe man bilicin ba.

Baya ga waɗannan, waɗanne dalilai ne kuke ganin suka sa waɗannan jaruman suke kaman ba sa tsufa?