| Hausa
SIYASA
1 minti karatu
China ta yi gargaɗin 'murƙushe' katsalandan ɗin ƙetare kan shirin makami mai linzani na Japan
Beijing tana ɗaukar Taiwan a matsayin ƙasarta kuma ba ta kawar da yiwuwar amfani da ƙarfi wajen mayar da ita ƙarƙashin ikonta ba.
China ta yi gargaɗin 'murƙushe' katsalandan ɗin ƙetare kan shirin makami mai linzani na Japan
Zane ya nuna tutocin China da na Taiwan / Reuters
26 Nuwamba 2025

China ta yi gargadi ranar Laraba cewa za ta “murƙushe” duk wani ƙoƙari na ƙetare na tsoma hannu kan batun Taiwan, bayan Japan ta yi shelar ajiye makamai masu linzami a kan wani tsibirin da ke kusa da Taiwan mai cin gashin kanta.

"Muna da ƙarfin zuciya da kuma jajircewa mai ƙarfi domin kare ‘yancinmu da kan iyakokinmu," in ji Peng Qingen, wani mai Magana da yawun ofishin China da ke sa ido kan harkokin Taiwan a wani taron maneman labarai cikin martaninsa ga wata tambaya kan shirin ƙaddamar da makaman.

"Za mu murƙushe tsoma baki na ƙetare."

Beijing tana ganin Taiwan a a matsayin ƙasarta kuma ba ta kawar da yiwuwar amfani da ƙarfi wajen karɓe iko da ita ba.

Gwamnatin tsibirin ta yi watsi da iƙirarin Beijing kan ikon da yankin, kuma ta ce ‘yan Taiwan kaɗai ne za su iya yanke hukunci kan makomarsu.

"Yadda Japan ta ƙaddamar da makamai a wuraren da ke kusa da yankin Taiwan na China don tsokana yana da matuƙar haɗari, abinda yake janyo tashin hankali a yankin da gangan da kuma neman arangamar soji," in ji Peng.

 

Rumbun Labarai
Shugaban Nijar ya ziyarci Aljeriya, lamarin da ya nuna ƙarshen tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen
Trump ya bar ƙofar Iran a bude, kuma Netanyahu ba zai iya rufe ta ba
Yadda 'yan Nijeriya suka fusata kan matakin Amurka na saka wa Kwankwaso takunkumi
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aika sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet
Taƙaddama a kan gyaran dokar zaɓe ta Nijeriya
Ghana ta yi wa jakadanta a Nijeriya kiranye kan zargin maguɗin zaɓe
Iran ta ce ta shiga tattaunawar Oman da Amurka da 'kyakkyawar niyya'
Masar da Saudiyya sun yi kira ga samar da hanyoyin da suka dace kafin tattaunawar Amurka da Iran
Greenland ba hajar sayarwa ba ce
Yayin da duniya ta koma kasuwar buƙatar diflomasiyya, wai zai tsaya wa ƙasashe marasa ƙarfi a 2026?
Amurka ta dakatar da bai wa ‘yan Nijeriya biza
Alkawarin dala miliyan 150 zai sake gina Aleppo da yaƙi ya lalata
Yadda 'nadamar zalunci' ke janyo rushewar lafiyar ƙwaƙwalwa a rundunar sojin Isra’ila
Me ya sa Trump da masu sharhi da ke da ra’ayin rikau ke sa ido kan al’ummar Somalia da ke Minnesota?
Shugaban Nijar Tiani ya karɓi shugaban Bilma bayan ya yi watanni 16 a hannun masu garkuwa da mutane
An daƙile harin RSF kan West Kordofan: Rundunar Sojin Sudan
Nijar ta ce ta fara kai uranium ɗinta kasuwar duniya
Trump ya ce Amurka za ta dakatar da hijirar 'yan cirani daga kasashe marasa arziki har abada
Gobarar Hong Kong: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 128 yayin da aka shiga kwana uku a ƙoƙarin ceto
Yaƙin Sudan: Maye gurbin UAE da Turkiyya na iya ƙarfafa ƙoƙarin ƙasashe na samar da zaman lafiya