Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya doke abokan hamayyarsa na Turai Lufthansa da Air France-KLM domin tabbatar da yarjejeniyar raba iko da kamfanin.

By
Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain

Kamfanin Jiragen Sama na Turkiyya ya sanya hannu kan yarjejeniyar sayen kashi daya bisa hudu na kamfanin jiragen saman Spain wato Air Europa, kamar yadda Turkish Airlines ya tabbatar a ranar Alhamis.

Turkish Airlines zai zuba hannun jarin da ya kai na dala miliyan 355, a karkashin yarjejeniyar da aka cim ma a watan Agusta.

Iyalan Hidalgo na Spain, ta hanyar Globalia, za su ci gaba da zama wadanda suka fi yawan hannun jari a kamfanin Europa, yayin da mamallakan British airways , AIG zai ci gaba da rike kashi 20 cikin 100 na jarin kamfanin ta hanyar sayen hannayen jarin a wajen Globalia.

Kamfanin jiragen saman Turkiyya ya doke abokan hamayyarsa na Turai Lufthansa da Air France-KLM domin tabbatar da yarjejeniyar raba iko da kamfanin jirgin tare da iyalan Hidalgo.

Turkish Airlines ya ce ba shi da shirin kara yawan hannun jarin.

Cinikin, wanda zai kammala da zarar an cika sharuddan dokoki cikin kimanin watanni 6 zuwa 12, ya kimanta darajar Air Europa a kusan Yuro biliyan 1.2 ($ biliyan 1.4).

Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da kamfanonin jiragen sama ke neman haɗa kasuwar nahiyar da ta wargaje ta hanyar ɗaukar ƙananan kamfanoni masu fama da matsaloli.

Bayan sanar da yarjejeniyar, Air Europa ta ce ta mayar da bashin kusan Yuro miliyan 500 (~$575 miliyan) daga kamfanin riƙon masana'antu na gwamnati na Spain SEPI shekara guda kafin lokacin da aka tsara.