Ghana na shirin kashe dala biliyan 3.4 a fannin makamashin da ake iya sabuntawa

Ministan makamashin ƙasar Ghana John Abdulai Jinapor ne ya bayyana wannan shirin ranar Laraba a taron makamashin da ake sabuntawa na Afirka (REFA 2025) da aka yi a birnin Accra.

By
Shirin na shekara biyar zai mayar da hankali ne kan samar makamashin da ake iya sabuntawa da ya kai megawat 1,400 a Ghana / Reuters

Gwamnatin ƙasar Ghana tana shirin kasancewa kan gaba a fannin makamashin da ake iya sabuntawa a nahiyar Afirka inda ta bayyana wani shiri mai cike da buri na saka jarin dala biliyan 3.4 a fannin makamashin da ake sabuntawa na ƙasar cikin shekaru biyar masu zuwa.

Ministan makamashin ƙasar John Abdulai Jinapor ne ya bayyana wannan shirin ranar Laraba a taron makamashin da ake sabuntawa na Afirka (REFA 2025) da aka yi a birnin Accra.

“Mun ɗauki matakai na jarumta domin haɓaka fannin makamashin da ake iya sabuntawa domin wadata a fannin tattalin arziki,” in ji ministan.

Shirin na shekara biyar zai mayar da hankali ne kan samar makamashin da ake iya sabuntawa da ya kai megawat 1,400 inda za a samar da ƙananan tashohin makamashi 400 da wuraren caji masu sauri 100 da kuma gaggauta samar da famfunan ban ruwa masu amfani da makamashin hasken rana domin tallafa wa harkar noma.

Jinapor ya kuma bayyana ci-gaban Ghana a fannin samar da makamashin da ake iya sabuntawa, yana mai cewa a halin yanzu ƙasar ce ke da farantin sola na saman kwano ɗaya tilo mafi girma a faɗin Afirka inda yake samar da megawat 16.8 na makamashi.

 Ya ƙara da cewa kwanan nan ne Shugaban John Mahama ya ƙaddamar da tashar makamashi ta sola mai iya samar da megawat 200 na makamashi wadda ake fatan faɗaɗa makamashinta zuwa megawat 1,000 nan da shekarar 2032.

Ministan ya bayyana irin arzikin da Afirka za ta iya samu a fannin makamashin da ake iya sabuntawa, yana mai cewa nahiyar tana da kashi 60 cikin 100 na arzikin makamashin hasken rana yayin da take fama da talaucin makamashi.

“Bai kamata nahiyar da ke da albarkar hasken rana mai yawa ta kasance cikin talaucin makamashi ba,” in ji shi.

“Bai kamata a lamunci hakan ba,” a cewarsa.

Ya yi kira ga gwamnatocin Afirka da masu zuba jari da shugabannin masana’antu na nahiyar su haɗa kai wajen tattalin makamashin da ake iya sabuntawa.

“Idan muka yi aiki tare wajen amfani da kashi 20 cikin 100 na makamashin da ake iya sabuntawa da muke iya samarwa, za mu iya kawar da talaucin makamashi tare da samar da ci-gaba mai ɗorewa a faɗin nahiyar,” in ji shi.