| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar taimakon China ko Rasha wajen kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Iran
Da yake magana gabanin wani taron ƙoli na ƙungiyar APEC ta ƙasashe uku a China, Trump ya ce Amurka ta raunata ƙarfin sojin Iran matuƙa, kuma tana da cikakken iko da Mashigar ruwan Hormuz.
Trump ya ce Amurka ba ta buƙatar taimakon China ko Rasha wajen kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Iran
Trump ya yi alkawarin kawo karshen yakin Iran 'nan ba da jimawa ba', kuma ya bayyana cewa ba zai nemi taimako daga China ko Rasha ba. / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington ba ta buƙatar taimakon China ko Rasha wajen kawo ƙarshen yaƙin da take yi da Iran, yana mai cewa dakarun ƙasarsa sun yi wa ƙarfin sojin Tehran mummunar illa.

Da yake magana gabanin wani taron ƙoli na ƙungiyar APEC ta ƙasashe uku a China, Trump ya ce Amurka ta raunata ƙarfin sojin Iran matuƙa, kuma tana da cikakken iko da Mashigar ruwan Hormuz.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Fox News a birnin Shenzhen na China a ranar Alhamis, jim kaɗan kafin ganawarsa ta ƙasashe uku da Shugaban China Xi Jinping da Shugaban Rasha Vladimir Putin.

"Ba ma buƙatar taimakon kowa. Mun karya ƙarfin rundunar sojin ruwan Iran, mun karya ƙarfin rundunar sojin sama, sannan mun lalata na'urorinta na kariya daga hare-haren sama," in ji Trump.

Ya kuma yi iƙirarin cewa yawan makamai masu linzami da Iran ke da su ya ragu zuwa kusan kashi 12 zuwa 13 cikin 100 daga na baya, yana mai cewa Tehran na son cim ma yarjejeniya da Amurka.

Yana ƙara da cewa "saboda haka, ba na buƙatar taimako, kuma ba zan je neman taimakon kowa ba."

Trump ya ce sojojin Amurka na da cikakken iko kan Mashigar ruwan Hormuz, yana mai cewa China da Rasha sun nuna kyakkyawar mu'amala da Washington, kuma sun ƙi tura jiragen yaƙin ruwansu zuwa yankunan da ake taƙaddama a kansu.

Cim ma yarjejeniya mai dorewa da Iran

Da yake magana kan tattaunawar da ake yi da Tehran, Trump ya yi iƙirarin cewa shugabannin Iran na neman a cim ma matsaya, amma shi yana son yarjejeniyar da za ta ɗore ta dogon lokaci.

"Zan kawo ƙarshen lamarin nan ba da jimawa ba. Ina nufin, ko ta wace hanya, za mu kawo ƙarshensa," in ji shi.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ganawa da Xi Jinping da Vladimir Putin a lokaci guda za ta amfani Amurka, Trump ya ce hakan na da muhimmanci ne saboda ƙasashen biyu suna aiki tare kuma suna da kyakkyawar alaƙa.

Ya zargi tsohon shugaban Amurka Barack Obama da haɗa kan China da Rasha saboda batun makamashi, yana mai cewa China na matuƙar buƙatar makamashi, yayin da Rasha ke da ɗimbin albarkatun makamashi.

Trump ya ƙara da cewa yana ganin Amurka na samun nasara a halin da ake ciki, yana mai cewa shugabannin ƙasashen biyu suna ƙaunarsa.

Game da rahotannin leken asiri da ke zargin Iran da shirin amfani da makamai masu guda wajen kai wa Washington DC hari, Trump ya ce akwai alamun Iran na nazarin amfani da makamai masu guba.

Yana mai cewa, "akwai alamun Iran na duba yiwuwar amfani da iskar gas da kuma makamai masu guda, Idan hakan ta faru, za mu murƙushe su gaba ɗaya."

Trump ya kuma musanta cewa wasu mambobin majalisarsa da ke zaune a sansanonin sojin Amurka sun koma can ne saboda barazanar da Iran ke yi.

Waɗannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin faɗa sakamakon yaƙin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, wanda ya janyo martanin hare-haren ramuwar gayya daga Tehran kan Isra'ila da ƙasashen yankin Gulf da ke karɓar sansanonin sojin Amurka.

An rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a watan Yuni, amma ba a aiwatar da ita gaba ɗaya ba sakamakon saɓanin da aka samu kan tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar ruwan Hormuz. An kuma ci gaba da samun arangama lokaci-lokaci tun daga watan Yuli.