| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Ambaliyar ruwa ta shafi fiye da mutum 110,346 — Gwamnatin Nijar
Kanar-Manjo Salissou Mahaman Salissou ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta bana ta shafi unguwanni 551 da ƙananan hukumomi 95 da kuma iyalai 15,177 a faɗin ƙasar Nijar.
Ambaliyar ruwa ta shafi fiye da mutum 110,346 — Gwamnatin Nijar
Ministan kayayyaki da ababen more rayuwa na ƙasar, Kanal-Manjo, Salissou Mahaman Salissou, ya bayyana halin da ake ciki kan ambaliya a ƙasar / ANP
29 Agusta 2025

Aƙalla mutum 110,346 ne ambaliyar ruwa ta shafa a cikin jihohi takwas na Jamhuriyar Nijar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, a cewar gwamnatin ƙasar.

Ministan kayayyaki da ababen more rayuwa na ƙasar kuma mataimakin shugaban kwamitin hana ambaliya na Nijar, Kanal-Manjo, Salissou Mahaman Salissou, ne ya bayyana wannan a lokacin da yake jagorantar zaman kwamitin a Yamai ranar Alhamis.

Kanar-Manjo Salissou Mahaman Salissou ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta bana ta shafi unguwanni 551 da ƙananan hukumomi 95 da kuma iyalai 15,177 a faɗin ƙasar Nijar.

Zaman kwamitin ya yi nazari game da irin gidajen da suka kamata a gina wa waɗanda ambaliyar ta fi shafa.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar ANP ya ambato mataimakin shugaban kwamitin yana tabbatar da cewa za ɗauki matakan da ya kamata domin tabbatar da cewa tallafi ya kai ga dukkan waɗanda ya kamata a bai wa.

A shekarar 2024 dai ambaliya ta kashe mutum  400 inda ta shafi mutum 1,501,634 daga iyalai 203,416 a faɗin ƙasar Nijar.