| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
ECOWAS ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafa wa aikin bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco
An tsara hanyar bututun ne don jigilar iskar gas mita cubic biliyan 30 (bcm) a shekara guda daga Nijeriya zuwa Marocco ta hanyar ƙasashe 13 da ke yankin yammacin Afirka, a cewar wata sanarwa haɗin gwiwa tsakanin Morocco da Nijeriya.
ECOWAS ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafa wa aikin bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco
An tsara hanyar bututun ne don jigilar iskar gas kyubik mita biliyan 30 a shekara guda daga Nijeriya zuwa Maroko

Mambobin ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) sun sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatoci ƙasashen a ranar Lahadi a Freetown don tallafa wa ayyukan bututun iskar gas na Nijeriya da Morocco Atlantic, a cewar wata sanarwar haɗin gwiwa tsakanin Maroko da Nijeriya.

An tsara hanyar bututun ne don jigilar iskar gas kyubik mita biliyan 30 (bcm) a shekara guda daga Nijeriya zuwa Maroko ta hanyar ƙasashe 13 da ke yammacin Afirka, a cewar sanarwar haɗin gwiwa wadda hukumar sinadarin hydrocarbon da haƙo mai ta Maroko ONHYM da kamfanin mai na Nijeriya NNPC suka fitar.

Daga cikin adadin, za a samar da kyubik mita 15 a kowace shekara ga kasuwannin Maroko da Turai ta hanyar bututun da ya haɗa Maroko da ƙasar Sifaniya, in ji sanarwar.

An amince da yarjejeniyar shekaru goma da suka wuce, tsakanin Sarkin Maroko da tsohon shugaban Nijeriya marigayi Muhammad Buhari, kuma an tsara bututun zai kai tsawon kilomita 6,900 kuma an ƙiyasta za a kashe dala biliyan 25 a aikin.

Tuni dai aka kammala matakin bincike da tsare-tsaren injiniyoyi a matakin farko (FEED) na aikin.

A watan Afrilu, ONHYM ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa an tsara aikin ne don haɓaka haɗin kan tattalin arziki a faɗin Yammacin Afirka ta hanyar faɗaɗa samar da wutar lantarki da kuma sauƙaƙa ci-gaban masana'antu da haƙar ma'adinai, tare da taimaka wa Maroko ta sanya kanta a matsayin hanyar makamashi tsakanin Afirka da Turai.

Mataki na gaba zai mayar da hankali kan sanya hannu a wata yarjejeniya tsakanin Maroko da Mauritania mai arzikin iskar gas a gaban shugaban Nijeriya, a cewar sanarwar.

Rumbun Labarai
Apple ya gabatar da iPhone Duo, wayarsa ta farko da ake rufewa
Aliko Dangote ya ƙaddamar da fara sayar da hannun-jarin matatar mansa ga jama'a
Uganda ta sanar da samun raguwar kaso 15% a hada-hadar fitar da kofi zuwa ƙasashen waje
Zuba jari a ɓangaren makamashi na Nijeriya na iya ƙaruwa cikin shekaru biyar – Hukumar IEA
Matatar Dangote ta Nijeriya za ta fara sayar da hannayen jari a karon farko nan da ‘yan kwanaki
Shirin bankin da ba ya karɓar ruwa ba don tallata wani addini ba ne – Gwamnan Babban Bankin Ghana
Trump ya soki Canada kan haraji cikin rigimar cinikayyar da Amurka ke yi da ƙasar
Kayan da Turkiyya ta fitar zuwa Afirka a 2026 sun haura na dala biliyan 13
Kuɗin Ghana ya koma fuskantar matsi, na Uganda na farfaɗowa, na Nijeriya zai iya sauyawa kaɗan
Amurka ta yi barazanar saka wa tattalin arzikin Iran takunkumin da 'duniya ba ta taɓa gani ba'
Gwamnatin Nijeriya za ta farfado da burtalan kiwo 417 a faɗin ƙasar
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Matatar Dangote ta fitar da tan fiye da 400,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yuli - Rahoto
Hukumar Kasuwanci Marar Shinge ta Afirka ta sanya hannu da wani kamfanin Nijeriya don inganta fito
A lokacin da cututtuka suka tsallaka iyaka: Manoman Afirka na neman sabbin matakan kariya
Farashin fetur a Amurka ya tashi sakamakon tsaiko a Hormuz da sanarwar Houthi ta rufe Bahar Maliya
Ƙungiyar EU ta sanar da sanya sabbin takunkumai kan cinikayyar zinare a Sudan
Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana ta ƙaru a wata uku a jere da 5.3% a Yunin 2026
Wa yake amfana a lokacin da tattalin arzikin duniya ke ci da wuta sakamakon yaƙi?
Abubuwan da dalar Amurka Tiriliyan 1.1 mallakin Elon Musk za ta iya yi a Afirka