Chadi za ta tura jami'an tsaronta 750 domin aiki a wani ɓangare na aikin tsaro da ke da goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) a Haiti, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta bayyana ranar Talata.
Haiti ta daɗe tana fama da ‘yandaba masu aikata laifuka .
A shekarar 2023, MDD ta amince da dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa domin taimaka wa rundunar ‘yansandan Haiti wajen fuskantar ‘yandaba, amma tura dakarun tsaron ya samu sakamako mai kyau da mara kyau.
A bara, kwamitin tsaro na MƊD ya amince da sauya aikin dakarun kiyaye zaman lafiyar zuwa wata rundunar mai ƙarfin tunkarar ‘yandaba.
Sojojin za su tafi Haiti a ƙarshen watan Maris
"Sojoji ɗari bakwai da hamsin a ƙarƙashin ‘yansanda da jandamari, za su haɗu da dakarun daƙile ‘yandaba bisa buƙatar MDD," kamar yadda wani hafsan sojin Chadi ya bayyana da sharaɗin sakaye sunansa. Ma’aikatar harkokin wajen Chadi ta kuma tabbatar da tura dakarun.
"Chadi ta amsa wani kira na MDD, wadda ta ce ita ƙasar za ta taka wata rawa ta sa ido da kuma ta jigila" ga dakarun daƙile ‘yandaba, in ji hafsan.
"An saka tafiyar kashi ta ɗaya cikin rundunar ne a ƙarshen watan Maris, kuma za a ci gaba da tura su har zuwa watan Yuni," in ji jami’in.
Sabuwar rundunar za ta iya samun jami’ai da mafi yawansu za su kai 5,500 masu kayan sarki, ciki har da ‘yansanda da sojoji.
Hare-haren ‘yandaba masu kisa
Za su maye gurbin aikin dakarun tsaro na ƙasa da ƙasa, wanda yawancin su ‘yansandan Kenya ne .
MDD ta bayyana ranar Talata cewa hare-haren ‘yandaba a Haiti da kuma ayyukan tsaro kan ‘yandaban sun janyo mace-mace 5,500 tsakanin watan Maris na shekarar da ta gabata zuwa tsakiyar watan Janairu.















