Ministan albarkatun man Nijar, Mr. Hamadou Tini ya gabatar da dabarun inganta fannin na ma’aikatarsa ranar Talata a gaban mambobin Majalisar ceto Ƙasa (CNSP) da sauran masu ruwa da tsaki.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Nijar ANP ya ruwaito cewa tsarin ya ƙunshi ɓangarori bakwai ciki har da inganta zuba jari kan neman mai da jagoranci tare da inganta samun abubuwa a harkar mai.
Har wa yau fannonin sun haɗa da ƙarfafa jagoranci da tsarin gudanrwa da samar da hukumar da za ta sa ido kan ɓangaren man Nijar (ɓangaren samo ɗanyen mai da ɓangaren raba tacaccan mai) wadda za ta yi aiki a matsayar mai tabbatar da doka a harkar tattalin arziƙi.
Waɗannan ɓangarorin sun haɗa da inganta kamfanoni na gida da ƙarewar ƙasar ; tattara ƙwarewar ƙasa da kuma buɗe ƙofa a hankali ga ƙwarewa na ƙetare da tsantsar bi a hankali da muhalli da kuma tasiri na kan zamantakewa da kuma bayyana gaskiya da mutane.
A jawabinsa ministan man ƙasar ya jaddada cewa wannan tsarin ya dace da tsare-tsaren kundin sake fasalin ƙasar wanda ya ba da fifiko kan ‘yancin tattalin arziki da shugabanci na gari da gaskiya da kuma inganta albarkatun ƙasa .
Ministan ya ƙara da cewa tsarin ya kuma ƙunshi dabaru da wasiƙr aiki ga ministan ta ƙunsa wadda ta nemi a ƙrafafa gudumowar fannin mai ga kuɗaɗen shigan ƙasar da inganta jagoranci da bayyana gaskiya da kuma inganta shiga ‘yan ƙasar harkar da kuma tafiyar da harkar ta hanya mai ɗorewa".

















