Me ya sa dokoki ke gaza bayar da kariya ga matan da ake yi wa auren wuri kuma na dole

Auren dole ya zama ruwan dare a wasu yankunan Afirka a yayinda talauci, camfi, rikicin sauyin yanayi da sakacin aiki da doka ke danne dokokin kariya, wanda ke jafa miliyoyin mata cikin zaman aure ala tilas da ke zuwa da munanan sakamamako a rayuwa.

By
Me ya sa dokoki ke gaza bayar da kariya ga matan da ake yi wa auren wuri kuma na dole / MSF

Maya tana ziyartar iyalinta don hutun Tabaski (Babbar Sallah) a ƙasarta ta asali Senegal lokacin da ta ji cewa mahaifinta ya yanke shawarar sake aurar da ta.

Labarin ya zo wa matar mai shekaru 30 da mamaki, bayan da ta kasa shawo kan wahalar da ta sha a lokacin da ta zama da wuri kuma ta riga ta haifi 'ya'ya biyu ita kaɗai.

Mutumin da aka zaɓa ya zama sabon mijinta, Mamadou B, abokin mahaifinta ne wanda ke zaune a Casamance a kudancin Senegal. Yana son Maya ta bar aikinta na mai kula da gida a Dakar ta haɗu da shi nan take. Za ta zama matarsa ​​ta uku.

"A lokacin auren dolena na farko shekaru 14 da suka gabata, ba ni da wani zaɓi illa in miƙa wuya ga shawarar mahaifina," Maya ta fada wa TRT Afrika. "Yana yanke manyan shawarwari a cikin iyalinmu, ko masu kyau ko marasa kyau."

Mijin Maya na farko shi ma abokin mahaifinta ne, mutum ne mai shekaru sittin.

A wannan karon, Maya tana fatan a ji ta bakinta. Za ta fi son yin aiki tukuru don renon 'ya'yanta maza biyu ita kaɗai da kuma sake gina rayuwarta fiye da a yi mata aure da wani mutum da ya kai shekarun mahaifinta.

Akwai miliyoyin labarai irin na Maya a faɗin Afirka, duk da dokokin ƙasa da kotunan Afirka da suka yi Allah wadai da auren dole.

Alkaluma masu tayar da hankali

Kusan ɗaya cikin mata uku an taɓa cin zarafinsu ta hanyar hantara ko ta hanyar jima'i aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu, a cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

Gangamin kwanaki 16 mai taken ‘UniTE’ don kawo ƙarshen cin zarafin mata, wanda aka ƙaddamar a ranar 25 ga Nuwamba da ya zo daidaita da Ranar Kawar da Cin Zarafin Mata ta Duniya, ya mayar da hankali kan yadda auren dole ya kasance babbar matsala a faɗin Afirka.

Masaniyar zamantakewa ta ƙasar Senegal Sely Ba ta yi nuni da cewa ɗaya cikin 'yan mata biyar a ƙasashe masu taso wa ana aurensu kafin su cika shekaru 18. Talauci ne ke haifar da yawancin waɗannan auren, kodayake al'adu da ƙabilu suma suna taka rawa.

A Sudan ta Kudu kaɗai, 'yan mata miliyan huɗu ne aka yi wa auren dole tun suna ƙanana ko kuma aka tilasta musu yin aure a shekarar 2022, wanda ya karu daga miliyan 2.7 a shekarar 2021, a cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

A duk duniya, UNICEF ta kiyasta cewa an yi auren dole miliyan 60 a shekarar 2022, inda Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka suka fi yawa. Gabon, Congo, Gambia, Burkina Faso, Najeriya, Chadi da Sierra Leone su ma suna cikin jerin kasashen da ke kan gaba.

Maya ta girma a cikin talauci a Casamance, wanda yanayi ya tilasta mata barin makarantar firamare ta zauna a gida don taimaka wa mahaifiyarta da ayyukan gida. Ba ta fita daga shekarun ƙuruciyarta ba lokacin da aka tilasta mata yin aure.

Da aka tambaye ta game da waɗannan shekaru 10, Maya ta yi shiru, saboda girmama tuna wa da mahaifin 'ya'yanta.

Ba ta bayyana cewa, "Yawan auren dole ya ninka sau uku a yankunan karkara fiye da na birane." "Waɗannan auren suna da yawan kashi 42.8% na dukkan auren da aka yi a yankunan karkara da kuma kashi 14.3% a yankunan birane."

A yawancin al'ummomin karkara, camfi yana taka rawa a cikin shawarwari kan ‘yan mata wadanda suka saɓa da lafiyar jiki da ta hankali.

Dangane da hulɗarta da waɗanda abin ya shafa da iyalansu, Ba, ta nuna cewa mutane da yawa suna ganin cewa aurar da 'ya'ya mata da wuri yana tabbatar da cewa an kare su daga alakar auratayya mai rikitarwa.

Sauyin yanayi shi ma ya bayyana a matsayin wani abu. UNICEF ta ƙara ganin fari na jefa iyalai cikin yanayin aurar da yara suna ƙanana.

"Muna ganin yawan auren yara ƙanana da kaciyar mata a faɗin yankin Afirka, inda wasu iyalai marasa galihu ke shirya wa 'yan mata 'yan shekara 12 su auri maza da suka ninka su shekaru har sau biyar," in ji Andy Brooks, mai ba da shawara ga UNICEF kan kare yara a gabas da kudancin Afirka, a cikin wani rahoto na 2022.

Matsalar aiwatarwa

Yawancin ƙasashen Afirka suna da dokoki da suka haramta auren dole. A shekarar 2021, kusan dukkansu sun amince da Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙin Ɗan Adam da na Jama'a da Haƙƙin Mata a Afirka.

Sashe na 21, sakin layi na 2 na Yarjejeniyar Afirka kan Haƙƙoƙin Yara da Jin Daɗin Yara, wanda aka gabatar a shekarar 1998, shi ma ya haramta auren dole.

Masana zamantakewa kamar Ba sun ɗora alhakin kan jinkirin aiwatar da doka maimakon rashin abubuwan da ke hana faruwar matsalar.

"Dukkan masu ruwa da tsaki a cikin al'umma dole ne su yi aiki don aiwatar wa da kuma girmama waɗannan dokoki don jindaɗin 'yanmatanmu da matanmu matasa," ta shaida wa TRT Afrika, tana mai ambaton ɗaukar ciki da matsalolin haihuwa da ke kashe iyaye mata da yawa.

Plan International sun bayar da rahoton cewa kusan 'yan mata miliyan 16 da da shekaru tsakanin 15 zuwa 19 suna haihuwa kowace shekara. Kimanin 'yan mata matasa 70,000 ke mutuwa kowace shekara sakamakon matsalolin da suka shafi ciki da haihuwa, inda auren dole ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da illolin.

Dan majalisar dokokin Congo Exaucé Ngambili Ibam ya ce hukumomin kasarsa suna daukar auren dole, galibi na 'yan mata ƙanana, a matsayin babbar matsala ta zamantakewa.

Dokar Mouebara ta Jamhuriyar Congo, wacce aka kafa a shekarar 2022 don hana wariya da kuma ƙara kariya daga cin zarafin mata, ta bayyana auren dole a matsayin tashin hankali. Sashe na 20 ya bayyana tashin hankalin zamantakewa a matsayin "bayyanar dangantaka da aka tsara kuma ta kafu a cikin al'umma wacce ke haifar da matsin lamba ko tilastawa a zamantakewar".

"Auren dole wani nau'i ne na tilasta wa a zamantakewa," in ji Ibam. "Duk wanda ya kuskura ya shiga irin wannan al'adar koma-baya game da mata zai fuskanci hukunci, wadda ba ta kyale kowa ba."

A Chadi, Burkina Faso da Senegal, akwai dokoki da ke hana auren dole bisa ga haƙƙin ɗan adam, da kuma saboda dalilai na lafiya da aminci. Masana zamantakewa, masana ilimin ɗan adam, likitoci da zaɓaɓɓun jami'ai suna kira ga hukumomi da su wayar da kan jama'a da kuma tabbatar da cewa an aiwatar da dokokin da ke akwai.

Ga Maya, makoma ta kasance cikin rudani. Dole ta bar aikinta a Dakar saboda matsin lamba daga iyali ta koma wani sabon gida a matsayin mata ta uku ga abokin mahaifinta Mamadou.