Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine

Ma’aikatar Harkokin Wajen Kamaru ta yi kira dga iyalan wadanda suka mutu da su tuntubi jami’an ma’aikatar a babban birnin Yaounde.

By
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine / Reuters

Kamaru ta ce hukumomin Rasha sun tabbatar da mutuwar 'yan Kamaru 16 da ke fafatawa da Ukraine, wannan shi ne karo na farko da kasar Afirka ta Tsakiya ta yi magana game da shigar 'yan kasarta cikin yaƙin da ake ci gaba da yi.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ta kafafen yada labarai na gwamnati a ranar Litinin da yamma, Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙasar ta yi kira ga iyalan wadanda suka mutu da su tuntubi jami'an ma'aikatar a babban birnin Yaounde.

Wata takardar saƙon diflomasiyya ta Kamaru, da aka fitar a ranar Litinin da Reuters ta gani, ta ambaci mamatan da “‘Yan kwangilar yaki ‘yan kasar Kamaru” a ke aiki a waje na musamman na ayyukan soji, salon da Rasha ke amfani da shi don bayyana yakin Ukraine.

Ba a fayyace ko kuma takardar diflomasiyya ba ta fayyace yadda mutanen 16 suka tsinci kansu suna yaki da Rasha, kuma ba su bayar da cikakkun bayanai kan wuri, lokaci da yanayin mutuwarsu ba.

Ofishin jakadancin Rasha da ke Yaounde bai bayar da amsa nan take ga bukatar Reuters ta yin tsokaci ba.

Daukar ‘yan Afirka su shiga yaƙi

A watan Fabrairu Ukraine ta ce sama da ‘yan Afirka 1,7000 na yaki tare da Rasha, mahukuntan Rasha sun musanta daukar mayaka daga Afirka ba bisa ka’ida ba don yaki a Ukraine.

A wata sanarwa ta cikin gida da akafitar a watan Maris din 2025 wadda Reuters ta gani, ministan tsaro na Kamaru ya bayyana damuwa kan cewa sojoji na barin kasar don zuwa shiga yaki a Ukraine inda ya ce kwamandoji sun sanya idanu sosai.

Kamaru ta ce a hukumance ba ta kai sojoji zuwa kasar waje ba in banda a ayyukan kasa da kasa ko na yankinta, kuma ta gargadi ‘yan kasar kan shiga yaki a wata kasar waje.