Attajirin Zimbabwe Wicknell Chivayo ya sake jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan ya yi tayin dala miliyan ɗaya ga fitaccen mawaƙi Thomas Mapfumo.
Ya yi tayin biyan dala miliyan ɗaya ga fitaccen mawaƙi Thomas Mapfumo domin ya yi waƙa a bikin ranar haihuwarsa da kuma bikin auren mawaƙi Jah Prayzah. Wato dala 500,000 ga kowane ɗaya daga cikin bukukuwan.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar 13 ga Yuli, ɗan kasuwar mai yawan janyo ce-ce-ku-ce ya ce hakan zai sa Mapfumo ya zama mawaƙin da aka taɓa biya kuɗi mafi yawa a tarihin Zimbabwe.
To, me ya sa Chivayo ke biyan kuɗi masu yawa haka domin wasanni biyu kacal – a bikin ranar haihuwa da na aure?
Attajirin ɗankasuwar na Zimbabwe, wanda aka fi sani da kusancinsa da shugabannin ƙasashen Afirka, ya ce wannan kuɗin wata girmamawa ce ga fitaccen mawaƙi Thomas Mapfumo, wanda aka fi sani da Mukanya.
Attajirin mai shekaru 43, wanda kasuwancinsa ya shafi makamashi da ababen more rayuwa, ya bayyana wannan kuɗin a matsayin "ƙaramar hanyarsa ta nuna godiya" ga Mapfumo saboda "gagarumar gudunmawar da ya bayar" ga masana'antar kiɗa da fasaha ta Zimbabwe.
Chivayo ya yaba wa Mapfumo musamman saboda "ƙwarin gwiwar" da ya bayar a lokacin gwagwarmayar neman 'yanci da kuma samun 'yancin kai na Zimbabwe, yana mai cewa waƙoƙinsa sun ilmantar, sun haɗa kan jama'a, kuma sun ƙarfafa zukatan al'ummomi da dama na Zimbabwe, sannan "tarihin gudunmawarsa zai ci gaba da rayuwa na shekaru masu zuwa."
Fitaccen mawaƙi
Chivayo, wanda aka haifa a ranar 22 ga Nuwamban 1982, ya byar da satar amsa kan cewa akwai yiwuwar a iya gudanar da wasan da fitaccen mawaƙin zai yi tsakanin tsakiyar watan Nuwamba da watan Disamba.
Mapfumo ya amince da tayin Chivayo ta wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce zai dawo Zimbabwe daga Amurka, inda yake zaune a halin yanzu.
Fitaccen mawaƙin mai shekaru 81 ya ce dawowarsa da yake shirin yi saboda aikinsa ne kawai, ba don wata manufar siyasa ba.
Thomas Mapfumo ya shafe shekaru da dama yana harkar kiɗa. Shi ne ya ƙirƙiro kuma ya shahara da salon kiɗan Chimurenga, wanda ke haɗa sautukan gargajiyar Zimbabwe da saƙonnin siyasa da zamantakewa.
Yana rera waƙa da harshen Shona cikin muryarsa ta musamman da salon waƙa mai tafiya a hankali amma mai ƙarfi. Mapfumo na ɗaya daga cikin manyan mawakan da suka taimaka wajen gwagwarmayar Zimbabwe na samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Bayan samun 'yancin kai a shekarar 1980, ya kuma sha samun saɓani da mahukunta kan batutuwan shugabanci a lokacin mulkin Robert Mugabe.
Yana zaune a Amurka tun shekarar 2005 bisa raɗin kansa, sai dai ya ziyarci ƙasar da ke kudancin Afirka a shekarar 2018 domin yin wani wasa.
















