Nijeriya na fuskantar yunwa mafi muni a tarihi saboda hare-haren ‘yan bindiga da rage tallafi: MDD

Kusan mutum miliyan ɗaya ne a ƙasar ta Afirka suke dogara da tallafin Hukumar Abinci Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), amma giɓin kudi ya tilasta wa hukumar rage shirinta na samar da abinci mai gina jiki a watan Yuli.

By
Kusan mutum miliyan 6 ba su da abinci mafi ƙaranci da suke buƙata a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe.

Ƙarin hare-haren ‘yan bindiga da kuma rashin tsaro na ƙara ta’azzara yunwa zuwa wani matakin da ba a taɓa gani ba a arewacin Nijeriya, a cewar Hukumar Abinci Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), inda ta yi gargadi ranar Talata cewa kusan mutum miliyan 35 za su iya fuskantar tamowa a shekarar 2026 yayin da kayayyakinta za su ƙare a watan Disamba.

Hasashen, bisa ma’aunin tsabar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankin Sahel da Yammacin Afirka, shi ne mafi girma da aka taɓa yi a Nijeriya tun lokacin da aka fara tattara bayanan, in ji WFP.

Rikici ya tsananta a shekarar 2025, inda ake fama da hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke da alaƙa da Alƙa’ida da ISWAP.

Ababen da suka faru kwanan sun nuna tsananin matsalar, inda mayaƙan ISWA suka kashe wani birgediya janar a arewa maso gabashin ƙasar, yayin da ‘yan bindiga suka saci ‘yan makaranta fiye da 300 a wata makarantar mabiya Ɗarikar Katolika ranar Juma’a, kwanaki bayan wasu ‘yan bindgia sun kutsa cikin makarantar gwamnati kuma suka sace ɗalibai ‘yan makaranta 25 ranar Litinin.

“Ƙaruwar tayar da ƙayar baya na mummunar barazana ga zaman lafiya a Arewa, lamarin da zai yi tasirin da zai tsallaka zuwa wajen Nijeriya,” in ji David Stevenson, daraktan WFP a Nijeriya. “al’ummomi suna cikin matsi mai tsanani daga hare-hare da kuma matsin tattalin arziƙi.”

Rashin abinci mai gina ya fi yawa ga ƙananan yara

Al’ummomin karkara manoma su ne lamarin ya fi shafa. Kusan mutum miliyan shida ne suka rasa abinci mafi ƙarancin da ya kamata su samu a jihohin Borno da Adamawa da Yobe, yayin da ake hasashen cewa kimanin mutane 15,000 za su fuskanci wani yanayi da ya yi kama da tsananin yunwa.

Matsalar rashin abinci gina jiki sun fi yawa ƙananan yara a jihohin Borno da Sokoto da Yobe da kuma Zamfara, a cewar WFP.

Kusan mutum miliyan ɗaya a arewa maso gabashin ƙasar a halin yanzu sun dogara ne kan tallafin WFP, amma giɓin kuɗin tallafin ya tilasta wa hukumar rage shirye-shiryenta na abinci mai gina jiki a watan Yuli, lamarin da ya shafi fiye da ƙannan yara 300,000. Rashin abinci mai gina jiki ya tsananta a wuraren da aka rufe asibitoci.

Wadda ta fi ba da tallafi, ƙasar Amurka, ta rage tallafinta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Donald Trump, kuma wasu muhimman ƙasashen ma sun rage ko kuma sun yi shelar rage tallafin.

WFP ta yi gargaɗin cewa za ta rasa kuɗin ba da agajin gaggawa na abinci cikin watan Disamba, lamarin da zai sa miliyoyin mutane da ke dogara kan tallafinta su rasa tallafi a shekarar 2026.