Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF a kusa da iyaka da Chadi

Rahotanni sun ce dakarun ƙungiyar RSF sun kutsa birnin El Tina, wanda ke gefen iyakar Sudan da Chadi, a ranar Asabar, amma sojojin na Sudan da haɗaƙar ƙawayensu sun tunkare su kuma suka ja da baya bayan arangama.

By
Sojojin Sudan da ƙungiyar RSF na yaƙi tun daga Afrilun shekarar 2023. / AP

Sojojin Sudan da haɗaƙar ƙawayensu sun daƙile wani hari da rundunar Rapid Support Forces (RSF) ta kai birnin El Tina da ke kan iyaka a Jihar Darfur ta Arewa.

Ƙungiyar agaji ta Coordination of Resistance Committees a Al Fasher a wata sanarwa ta bayyana cewa dakarun ƙungiyar RSF sun kutsa El Tina, wanda ke gefen iyakar Sudan da Chadi, a ranar Asabar, amma sojojin na Sudan da haɗaƙar ƙawayensu sun tunkare su kuma suka ja da baya bayan arangama.

Ƙungiyar ta ce dakarun waɗanda ke kai hari sun janye a lokacin da aka fara musayar wuta a birnin.

Gwamnan yankin Darfur, Minni Arko Minawi, ya bayyana harin RSF a El Tina a matsayin “kai hari ga fararen-hula marasa makami da aikata laifi.”

A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, ya saka bidiyoyi da ke ikirarin yadda dakarun na haɗaka ke ƙwace motocin RSF da makamansu a El Tina.

Matsalar jin kai mafi tsanani

Mayaka masu goyon bayan sojojin Sudan sun rinƙa yaɗa bidiyoyi a kafafen sada zumunta daga cikin garin, suna nuna motocin yaƙi da suka lalace, makamai, da mutanen da suka bayyana a matsayin fursunonin RSF.

A safiyar ranar Asabar, RSF a wata sanarwa a tashar ta ta Telegram ta bayyana cewa ta kwace iko da El Tina.

Daga cikin jahohin Sudan 18, RSF na rike da jihohin Darfur guda biyar a yammaci, sai dai wasu sassan Darfur ta Arewa da sojoji ke rike da su. Sojan kasa na riƙe da mafi yawan sauran jihohi, ciki har da babban birnin Khartoum.

Darfur na da kusan kashi ɗaya cikin biyar na yankin Sudan mai fiye da murabba'i kilomita miliyan 1.8, duk da haka mafi yawan mutane daga kimanin miliyan 50 na ƙasar na zaune a wuraren da soja ke iko da su.

Yakin da ya fara a watan Afrilun 2023 ya kashe dubban mutane kuma ya tilasta wa kusan mutum miliyan 13 barin matsuguninsu, da haifar da ɗaya daga cikin mafi munanan rikice-rikicen jin kai da yunwa a duniya, kamar yadda rahotannin Majalisar Dinkin Duniya suka nuna.