Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a ranar Litinin ta ce ta soke biza fiye da 100,000 tun bayan dawowar Trump, wani tarihi na shekara guda.
Amurka ta ce a ranar Laraba ta dakatar da aiwatar da bizar baƙi daga Nijeriya da wasu ƙasashe 74, matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka kan baƙi da ke son zuwa Amurka.
"Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta dakatar da aiwatar da takardar izinin shigar ƙasar ga ƙasashe 75," in ji wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Sakatariyar Yaɗa Labarai ta Fadar White House Karoline Leavitt ta wallafa a shafinta na X cewa ƙasashen da abin ya shafa za su haɗa da Somaliya - wadda Trump ya dinga caccakarta cikin yanayi mai tsananin a baya bayan nan bayan da aka samu baƙin-haure da badakalar kuɗi a Minnesota - da kuma Rasha da Iran.
Leavitt ya wallafa wani labari na gidan talabijin na Fox News wanda ya ce sauran kasashen da abin ya shafa za su hada da wasu kasashe da ke da dangantaka ta abokantaka da Amurka, ciki har da Brazil, Masar da Thailand.
Trump bai ɓoye burinsa na rage yawan shige da fice daga mutanen da ba 'yan asalin Turai ba. Ya bayyana 'yan Somaliya a matsayin "shara" waɗanda ya kamata su "koma inda suka fito" kuma maimakon haka ya ce yana maraba da 'yan yankin Scandinavia wato Denmark, Norway, da Sweden da ke ƙaura zuwa Amurka.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka a ranar Litinin ta ce ta soke biza fiye da 100,000 tun bayan dawowar Trump, wani tarihi na shekara guda.
Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta ce a watan da ya gabata gwamnatin Trump ta kori fiye da mutum 605,000, kuma wasu miliyan 2.5 sun tafi da kansu.
Wannan sabon matakin bai shafi bizar yawon bude ido ko ta kasuwanci ba, duk da cewa gwamnatin Trump ta yi alƙawarin tantance tarihin duk masu neman shiga shafukan sada zumunta.