Gwamnonin arewacin Nijeriya na neman a dakatar da haƙar ma’adinai domin matsalar tsaro
Gwamnonin arewacin Nijeriya, waɗanda suka sha alwashin kafa asusun tsaro na naira biliyan ɗaya, sun kuma tabbatar da goyon bayansu ga ƙoƙarin samar da tsarin ‘yan sanda na jihohi.
Gwamnonin jihohin arewacin Nijeriya 19 da sarakunan gargajiya sun yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya dakatar da haƙar ma’adanai na tsawon watanni shida a cikin matakan daƙile fashin daji da kuma aika-aikar ƙungiyoyin da ke aikata laifuka.
Shugabannin, waɗanda suka sha alwashin kafa asusun tsaro na naira biliyan ɗaya, sun kuma tabbatar da goyon bayansu ga ƙoƙarin samar da tsarin ‘yan sanda na jihohi.
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Nijeriya (NSGF) da kuma majalisar sarakunan gargajiya ta arewacin Nijeriya sun zauna ne a ɗakin taron Sir Kashim Ibrahim House, da ke Kaduna, ranar Litinin domin tattaunawa kan ƙaruwar hare-haren masu tayar da ƙayar baya da suka addabi yankin.
A cikin ‘yan watannin nan, kaɗan ne daga cikin jihohi 19 na arewacin ƙasar suka tsira daga hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, wanda ya karanta jawabin bayan taro, ya bayyana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a matsayin muhimmin abin da ke haddasa rashin tsaro kuma yake taimaka wa ƙungiyoyin ‘yan bindiga tare da lalata ƙauyuka.
Gwamnonin sun yi kira ga shugaban ƙasar ya bai wa ma’aikatar ma’adinai umarnin dakatar da lasisin haƙar ma’adinai na wata shida.
Gwamna Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin na NGSF, ya ce ƙungiyar ta nuna damuwa matuƙa game da kashe-kashe na baya bayan nan da kuma garkuwa da mutane da yawa da aka yi a jihohin Kebbi da Kwara da Kogi da Neja da Sokoto da Jigawa da kuma Kano, tare da sabbin hare-haren Boko Haram a Borno da Yobe, kuma ya miƙa saƙon ta’aziyyarsu ga iyalan da lamarin ya shafa.
Ƙungiyar ta yaba da matakin da Shugaba Tinubu ya ɗauka nan-take wajen ganin an dawo da wasu daga cikin yaran da aka yi garkuwa da kuma yadda hukumomin tsaro suke yaƙar masu tayar da ƙayar baya.
Yahaya ya ce a haɗe kan yankin yake wajen goyon bayan duk wani muhimmin mataki na murƙushe masu aikata laifuka.
Ya ce gwamnonin da sarakunan suna goyon bayan yunƙurin ba da damar kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai kira ga ‘yan majalisu dokoki daga arewacin ƙasar su aiwatar da sauyin kundin tsarin mulkin da zai kawo shi.