Wane tasiri shigar Yusuf Buhari siyasar Nijeriya za ta yi?

Yusuf ya bayyana wannan sha’awa ne a wata wasiƙa da ya rubuta ranar 3 ga watan Afrilu, 2026, inda ya ce yana son tsayawa takarar kujerar ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’Adua a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

By
Yusuf Buhari / Nigeria Presidency

Shin zai yi kamar mahaifinsa, Muhammadu Buhari? Wannan ita ce tambayar da ake ta maimaitawa bayan ɗa namiji ɗaya tilo ga tsohon shugaban Nijeriya, marigayi Muhammadu Buhari, wato Yusuf Buhari ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar ɗan Majalisar Wakilai ta ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Yusuf ya bayyana wannan sha’awa ne a wata wasiƙa da ya rubuta ranar 3 ga watan Afrilu, 2026, inda ya ce yana son tsayawa takarar kujerar ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’Adua a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Nuna sha’awar tasa na zuwa ne mako guda bayan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Sandamu, jihar Katsina, sun bayyana goyon bayansu gare shi a matsayin ɗan takarar da suka fi so ya wakilci mazaɓar Daura/Sandamu/Mai’Adua a Majalisar Wakilai.

An cim ma wannan matsaya ne a wani zama da aka gudanar a Sandamu, wanda ya haɗa zaɓaɓɓun jami’ai na tarayya da kuma waɗanda aka naɗa a muƙaman gwamnatin tarayya daga yankin.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ƙaramar hukumar, Usman Na-Lado, ya bayyana goyon bayan a matsayin matsaya ta gamayya da masu ruwa da tsaki suka amince da ita. Ya ce ƙwarewa da kuma karɓuwar da Yusuf ke da ita a cikin jam’iyyar ne suka sa ake ganin ya dace da takarar.

Wane tasiri zai yi?

Sai dai tambaya ita ce: wane irin tasiri takarar Yusuf Buhari za ta yi a siyasar Nijeriya?

Ba a fara jin duriyar Yusuf Buhari da sauran ‘yanuwansa ba sai a lokacin zaɓen 2015, duk da cewa mahaifinsa ya shafe shekaru yana neman shugabancin ƙasa kafin nan. A wancan lokaci ma, an fi jin sunan Zahra Buhari fiye da Yusuf, wanda aka fi sani da halin shiru-shiru.

Ana ganin hatsarin babur da ya yi a shekarar 2017, inda ya ji rauni a kai, shi ne ya fara fito da shi fili a idon jama’a.

Sannan kuma ana ganin cewa hidimar aurensa da aka gudanar a shekarar 2021 ta sake fito da shi a idon jama’a, sakamakon yadda auren ya kasance na alfarma, wanda ya tara manyan masu mulki da ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Bayan rasuwar mahaifinsa kuma, sunansa ya sake fitowa, musamman yadda ya taka rawa a shirye-shiryen jana’iza, karɓar gaisuwa, da kuma jawabin godiya da ya gabatar ga Shugaba Bola Tinubu a taron majalisar zartarwa ta ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa.

A wasiƙar ayyana aniyar tasa, Yusuf ya bayyana cewa burinsa na zama ɗan Majalisa shi ne samar da ayyukan raya ƙasa, tallafa wa al’umma, da kawo ci gaba ga mutanen mazaɓarsa.

Shin zai kai matsayin mahaifinsa?

Marigayi Muhammadu Buhari ya yi farin jini sosai, har ana ganin babu ɗan siyasar da ya kai irin nasa a tarihin Nijeriya, musamman bayan nasarar da ya samu a kan Goodluck Jonathan a zaɓen 2015.

Halayen da ake alaƙanta marigayi Buhari da su na ƙyamar cin hanci da rashawa da gaskiya da riƙon amana su ne ginshiƙin farin jininsa.

Duk da cewa bayan ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas da kuma rasuwarsa, ra’ayoyi sun rabu—inda wasu ke sukar mulkinsa, yayin da wasu ke yabonsa a matsayin shugaba mai gaskiya da adalci.

A yanzu haka, tambayar da ake yi ita ce: shin nawa daga cikin farin jinin mahaifinsa ne Yusuf Buhari zai amfana da shi a zaɓen 2027?

Masu sharhi suna ganin zai yi wahala Yusuf ya samu irin farin jinin mahaifinsa musamman a yanayin siyasar zamanin nan ta Nijeriya, sai dai masu magana kan ce albarkacin kaza, ƙadangare kan sha ruwa kasko.

Yanzu tambayar da ku za ku yi nazarinta ita ce, wane mataki zai iya kaiwa a siyasa, kuma wace irin rawa zai taka a nan gaba?