Gwamnatin Nijar ta zartar da dokar tilasta wa 'yan ƙasar shiga aikin soja
Dokar za ta buƙaci ‘yan ƙasar Nijar su gaggauta amsa kiran tafiya fagen yaƙi domin kare ƙasarsu da zarar an buƙaci hakan daga gare su.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ranar Jumma’a ta zartar da wata dokar soji da ta tilasta wa ‘yan ƙasar shiga aikin soji domin kare ƙasar daga barazana daga ciki da wajen ƙasar.
An amince da dokar ce lokacin Taron Majalisar Ministoci wadda shugaban ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ya jagoranta.
Majalisar ta fitar a ƙa’idoji na aiwatar da wannan doka.
Dokar za ta buƙaci ‘yan ƙasar su gaggauta amsa kiran tafiya fagen yaƙi domin kare ƙasarsu da zarar an buƙaci hakan daga gare su.
Sannan su miƙa bayanai ga hukumomi da zarar sun ga wani ɗan wata ƙasar waje da ke barazana ga Nijar, kana su guji yin duk wata sadarwa da za ta iya yin zagon-ƙasa ga yunƙurin zuwa fagen daga.
Kazalika hukumomin ƙasar suna shirin ƙaddamar da wani gagarumin wayar da kan jama’a a faɗin Nijar da zummar ƙarfafa kishin ƙasa da fayyace irin rawar da ‘yan ƙasar za su taka domin ci-gabanta.
Ƙalubalen tsaro
Wannan mataki na zuwa ne a yayin da Jamhuiyar Nijar ke ci gaba da fama da hare-haren masu tayar da ƙayar baya waɗanda suka addabi yankin Sahel da kuma ƙoƙarin ƙasar da maƙotanta na yin haɗin gwiwa domin kyautata tsaro a tsakaninsu.
A ranar 20 ga watan Disamba, ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES), da ta haɗa Nijar, Mali, da Burkina Faso, ta ƙaddamar da rundunar soji ta haɗin gwiwa mai ƙarfin soji 5,000-wadda ake kira United Force of the AES (FU-AES).
An ƙaddamar da rundunar ce a Bamako wanda shugaban Mali Assimi Goita ya jagoranta. Wani babban jami’in sojin Burkina Faso Janar Daouda Traore ne zai jagorance ta kuma tana da hedkwata a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.
Babban aikin rundunar shi ne yaƙi da ta’addanci da inganta tsaron iyakokin ƙasashen da kyautata musayar bayanan sirri tsakanin ƙasashen uku.
Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar suna ci gaba da ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu tun bayan ficewarsu daga ƙungiyar ECOWAS.